Connect with us

MANYAN LABARAI

Hukumar FRSC Ta Yi Wa Jami’anta 20 Karin Girma

Published

on

A jiya Juma’a ne hukumar kula da hadurra ta kasa wato FRSC, ta amince da karin mukami ga wasu jami’anta su 20, takwas daga cikin su kwamandojin hukumar ne, a yayin da 12 kuwa mataimakan kwamandoji ne.

Kwamandoji takwas din an kara musu mukami zuwa Mashal, su kuma mataimakan kwamandoji 12 din an kara musu mukami zuwa kwamandojin hukumar.

Jami’in huldar wayar da kan jama’a na hukumar Bisi Kazeem ya ce, shugaban kwamitin hukumar, Barista Bukhari Bello, ya yaba da yadda hukumar ta ke aiki ba nuku-nuku, sannan ya tabbatar da cancantar wadanda aka kara wa mukamin.

Jami’an sun yi alkawarin ci gaba da yin aiki tukuru, sun koma yi alkawarin samar da walwala da jin dadin aiki ga sauran jami’an da suke kasa da su.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: