Mustapha Ibrahim" />

Hukumar Hajji Ta Zama ’Yar Lele A Wurin Gwamna Ganduje – Abba Dambatta

Babban Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya bayyana cewa, Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na da kudiri da buri na ganin an samu nasara a aikin Hajjin bana kamar yadda aka samu a bara, inda aka samu kyaututtuka daga Hukumar jami`an tsaro ta farin kaya da kungiyar `’Yan Jaridu masu dauko labaran aikin Hajji ta kasa da kuma ita kanta Hukumar Alhazan ta kasa wacce ta baiwa Hukumar Alhazan Kano kyautar lambar yabo a kan tsabtar muhalli, abinci, da`a, bin dokokin kasa da kuma tafiyar da aiki daidai da aikin Hajjin.

Wannan ya samu ne sakamakon kulawa da goyon bayan da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje yake baiwa wannan Hukuma ta Alhazai, wacce ya ke kulawa da ita  da hakan ya sanya muka zama tamkar wasu `yan lele a cewar Sakataren Hukumar Alhazan, Malam Muhammad Abba Danbatta.

Haka kuma, ya ce yanzu haka kusan saura `yan kwanaki kadan a fara tashi zuwa kasa mai tsarki, wanda maniyyata za su fara shiga Saudiyya a ranar 6 ga watan Yulin 2019 a fadin duniya baki daya.

Kazalika, a nan Nijeriya za mu fara tashi a ranar 10 ga watan Yulin 2019, wanda a yanzu haka mun kammala aikinmu kusan kashi 75 cikin 100, na shirye-shirye Hajjin bana, mu ne kuma a kan gaba wajen yin bitar Alhazai, inda muke daukar kimanin watanni bakwai ana yi a shiyyoyi 32 da kuma bayyana ilmin aikin Hajji a kafafen yada labarai masu yawa a Kano, wanda duk wani mataki na samu ingancin aikin Hajji da mai girma gwamnan Kano ya dauka na samun nasara.

Yanzu haka dai maniyata daga Jihar Kano za su biya kudin aikin hajji na bana a kan kudi Naira 1,533,575, wanda kuma shi ne aka karkare na dukkanin hidindimun da za a yi wa kowanne maniyaci,0 kamar yadda kowace jiha ita ce ke da alhakin bayyana aikin Hajjinta gwargwadon nisanta da kuma ayyukan su ga maniyyatansu.

A karshe, ya bayyana cewa za a dauki ma`aikata masu taimakawa maniyyata a kasar Saudiyya gwargwadon yawan maniyyata da kuma irin bukatar aikin ma`aikata ga maniyyatan a can kasar ta Saudiyya, wanda a bara Hukumar jin dadin alhazan Jihar kano na da kujeru 5005, inda a bana ma haka Hukumar Alhazan ta kasa ta baiwa Kano wannan adadi, sanin kowa ne Kano ta samu gagarumar nasara a aikin Hajjin da ya gabata na 2018. Rahotannin sun tabbatar da cewa, Hukumar alhazai ta Kano ta rufe karbar kudin aikin Hajji na bana a ranar Juma`ar da ta gabata.

Exit mobile version