Daga Abubakar Abba, Kaduna
Hukumar Hana Shige da Fice taja kunnen ‘yan Nijeriya da kada su yi tafiya zuwa kasar Jamani ko sauran kasashen waje ta haramtacciyar hanya, ganin cewar, kashi tsa’in na ma su yin tafiya kasashen wajen, su na tafiya ne harmtacciyar hanya da a yanzu suke yin gudun hijira, hukumomin nahiyar Kasar Turai sunki ki amsar su.
Mataimakiyar Kwantilorar Hukumar, Sadat Hassan ce ta yi wannan gargadin a taron wayar da kai da hukumar ta gudanar a Jihar Legas.
Sadat ta shawarci ‘yan Nijeriya dasu tabbatar da sun samu dukkan takardun izinin fita kasashen waje da suka wajaba kafin su fice zuwa kasar ta Jamani da kuma sauran kasashen nahiyar Turai.
Rita ta koka akan ganin mafi yawancin bakin hauren daga kasar nan, mata ne wadanda kuma masu daukar nauyin su zuwa kashen wajen, suke bugewa yi ma su fyade a can kasashen wajen ko kuma tursasa su shiga karuwanci.
Ta kara da kokawa da cewar, mafi ya wancn ‘yan Nijeriya da ake koyo wa daga kasashen wajen, suna dawo gida dauke da cutar Kanjamau, wasu kuma ana cire wasu sassan jikin su a saida a kasuwar bayan fage.
‘Yar Majalisar ta shawarci ‘yan Nijeriya ma su sun zuwa kasashen ketare da su nemi sanin makasudin tafiyar da su kasashen waje daga ma su son daukar nauyin su, don gudun kada ma su son daukar nauyin nasu, su yi amfani da damar su muzgunawa rayuwar su.
Rita ta yi kira ga iyaye da da dangi da kada su matsa sai sun kai ‘ya’yan su zuwa kasashen waje don gudun kaucewa jefa rayuwar su cikin hadari.
Ta yi nuni da cewar, wasu na ganin wani aji ne ‘ya’yan suje kasashen ketare, wasu ma har filayen su da gonan su suke sayar wa da kayan su ma su tsada don su tura ‘ya’yan su kasashen waje, ba tare da sanin me yasa ‘yan nasu zasu je kasa shen ketaren ba.
Ta ce, idan suka samu nasarar tsallaka kasashen wajen, su na shiga cikin tasko iri-iri da baza su iya jure wa ba, saboda sun shiga ne a matsayn bakin haure, wasu sukan buge da yiwa jami’an tsaron kasashen wajen da suka kama su karya, inda kuma babu wanda zai iya basu wata kariya a can akan halin da suka shiga.
A nashi jawabin Shugaban kungiyar Femi Awoniyi ya bayyana cewar, akwai kimanin ‘yan Nijeriya su dubu sha biyu da aka kama a bisa tsallakawa kasashen ketare ba bisa ka’ida ba, da gwamnatin kasar Jamani taki
Ya bayyana cewa, a bisa kididdigar da Hukumar Hana Bakin Haure tsallakawa Kasashen waje ta ta duniya ta bayar ya nuna cewar, a kalla bakin haure su 2,500 ne suka mutu a kan Babban gulbin Mediterranean, inda kuma anyi amannar wasu sun mutu a cikin Sahara lokacin da suke kanyar su ta zuwa kasar Libiya.
Femi a karshe ya bayyana cewar, mafi yawancinsu sun fita ne ta baraunyar hanya.