Connect with us

LABARAI

Hukumar Hisba Ta Damke Gandaye A Kano

Published

on

A kokarin da Hukumar Hisba ta Jihar

Kano ke yi na ganin al’ummma na biyayya

ga dokokin Allah, a jiya Alhamis daya ga

watan Ramadan wanda galibin al’ummar

Musulmi a fadin duniya suka fara aiwatar

da daya daga cikin rukunan Musulunci na

zumi ta damke Gandaye wadanda suka

keta alfarmar watan.

Tun da farar safiyar ranar rundunar

Hisban ta kai samame domin damke

Gandayen a Unguwar Sabon gari da wasu

sassa na Jihar Kano da ake gudanar da

kasuwar tsaye.

Tawagar Jami’an Hisbar sun yiwa

wasu layukan Sabon Gari dirar Mikiya,

wanda hakan ya ba su sa’ar cika hannu da

Gandaye Goma maza da kuma mace guda

daya.

Wakazalika, daga Sabon Garin, jami’an

Hisba a karkashin jagorancin Muhammad

Tasi’u Muhammad suka nausa zuwa

Unguwar Fagge inda masu irin wannan

halin suka tsere ba a samu damke ko guda

daga cikinsu ba.
Da yake karin haske ga manema

labarai, Babban Darakta

Hukumar Hisba ta Jihar Kano,

Malam Abba Sa’id Sufi ya jinjina

wa jami’an da aka dora wa

alhakin damke Gandayen bisa

wannan kokari wanda ya ce ba

abin mamaki ba ne idan aka yi

la’akari da zakakuran ma’aikatan

hukumar.

Daga ya yi doguwar nasiha

ga masu irin wannan hali da

cewar su ji tsoran Allah, ya kuma

tabbbatar masu da cewa duk

inda suka buya Allah na ganinsu.

A karshe Abba Sufi ya taya

al’ummar musulmi murnar

shiga wannan wata

mai alfarma tare da yin

addu’ar Allah ya karbi ibadunmu.

Hakazalika

Sufi ya jijinawa Gwamna

Ganduje bisa fitar da miliyoyin

Nairori domin ciyar da marasa

galihu a Jihar Kano .
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: