Daga Umar Faruk, Birnin Kebbi
Biyo bayan hadarin jirgin kwale-kwalen da ake yawan samu a kogin Neja a Jihar Kebbi, Hukumar Kula da Wutar Lantarki da Ruwan Kogi ta kasa (HYPPADEC), ta raba rigunan shiga jirgen ruwa ga matukan jirgin ruwa na masarautun Gwandu, Argungu da Yauri har guda dubu goma (10,000) da nufin dakile asarar rayuka da ake samu kan hadurran jirgen kwale kwale a yankin.
A watan Yunin shekarar da ta gabata ne wani jirgin ruwa da ya taso daga Jihar Neja zuwa Jihar Kebbi dauke da ‘yan kasuwa da masu aikin hakar ma’adinai ya kife, inda ya kashe mutane kusan 100 a lokacin.
Manajan Daraktan HYPPADEC, Sadik Abubakar Yelwa ya bayyana haka ne a wurin bikin raba Rigunan shiga ruwan kogi a jirgin kwale kwale a fadar mai martaba Sarkin Yauri Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi. A lokacin da yake raba wa masu amfani da hanyoyin ruwa ta hannun sarakunan gargajiya a garin Yauri hedikwatar karamar hukumar Yauri inda ya ce, zabin raba rigunan a garin Yauri shi ne don an yi la’akari da yawaitar hadurran ruwa a yankin ya zarce abin da ake yi a duk jihohi shidan da hukumar ta kafa.
Ya kara da cewa, an kuma fara shirin samar da karin 20,000 na Rigunan ‘Life jackets’ don rabawa a jihar inda ya kara da cewa shawarar karin kayan ya zama dole idan aka yi la’akari da yawan hadurran da ke faruwa a duk lokacin da suka faru.
Shugaban hukumar HYPPADEC Sadik Yelwa, ya kuma kara da cewa hukumarsa ta fara aikin kawar da baragurbin ruwan da ke haddasa mafi yawan hadurran inda ya ce, an cire katako da tarkacen da ke karkashin ruwan yayin da ake shirin kwashe duwatsun karkashin ruwa.
“Jihar Kebbi ce ta fi kowace jiha yawan aukuwar hadarin kwale-kwale a jihohi shida da suka hada da HYPPADEC, bayan cire itatuwan da ke karkashin ruwa da kuma itacen da ke haifar da hadari ga harkar safarar ruwa, mun kai ga yanke shawarar raba Rigunan shiga ruwan kogi da ake kira a turance live jackets don kariyar hatsari na gaggawa yayin tafiya cikin jirgin kwale kwale, wanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da shi wanda ke dauke da rigar ceto zai iya yin iyo na tsawon sa’o’i shida a cikin abin da aikin ceto zai iya zuwa.”
A nasa jawabin, Sarkin Yauri, Muhammad Zayyanu Abdullahi, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa yadda ta tabbatar da cewa kungiyar HYPPADEC ta fara aiki, inda ya ce, a cikin kankanin lokaci da ta dauki matakan da suka dace musamman, masu safarar jiragen ruwa sun shigo cikin wasa.
“Muna matukar godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin tabbatar da cewa hukumar ta fara aiki kuma a cikin gajeren lokaci hukumar ta fara gudanar da ayyuka masu kyau. Tsaro shi ne babban abin da ya shafi harkar sufurin ruwa kuma a nan ne HYPPADEC ta sanya a gaba.”