Hukumar ICPC Ta Shirya Taron Horar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Kano Sanin Makamar Aiki

Daga: Mustapha Ibrahim, Kano

Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta shirya taron horar da shugabannin Kananan Hukumomin Kano da mataimakan su da Sakatarori horan sanin makamar aiki ta yadda zasu tafi da ayyukan sub a tare da wasu matsaloli ba domin dai yin aiki cikin ka’ida ta hanyar dokoki da aka tsara wajan gudanar da ayyuka a matakan Kananan Hukumomi kamar yadda ya ke a tsare.

A jawabin sa shugaban kungiyar shugabannin Kananan Hukumomi na ALGON na Kano Honorabul Laminu Sani Kawaji ya bayyana gamsuwar sa akan wannan taro da wannan hukuma ta shirya kuma yayi alwashin yin aiki da duk kanin ka’idojin gabatar da aiki a matakan Kananan hukumomi Kano bisa jagorancin shugaban su kuma Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A karshe ya bayyana cewa yanzu haka Kananan Hukumomi 44 na Kano kowacce na iya kokarin ta da kuma yin ayyuka gwargwadon abinda za ta iya yi a matsayin ta na karamar Hukuma haka kuma ALGON Honorabul Laminu Sani ya yabawa kwamishinan Kananan Hukumomi na Jahar Kano Honorabul Murtala Sulan Garo akan hadin kai da yake ba shugabannin Kananan Hukumomi 44 na Kano.

Exit mobile version