Hukumar INEC Ta Gargadi Atiku da Bindow

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta gargadi tsohon mataimakin Shugabancin kasa Alhaji Atiku Abubakar da gwamnan jihar Adamawa Mohammed Jibrilla Bindow a kan allunan yakin neman zabensu da aka kafe a wurare daban daban a fadin Jihar, “Wannan ya sabawa dokokin zabe” in ji INEC.

Shugaban Hukumar INEC ta jihar Adamawa Malam Kassim Gaidam, ya yi wannan bayanin a wajen taron masu ruwa da tsaki a harkar zabe a jihar, ya ce, mutanen biyu sun fantsama yakin neman zabe ta hanyar kakkafa allunan yakin neman zabe tun kafin a buga gangan siyasar.

A kan dan gyare gyraen da majalisar tarayya ta yi a kan tsarin gudanar da zabe, ya ce, tsarin da hukumar INEC ta fitar na nan daram kuma babu wani doka da ya hana ta tsara yadda za a gudanar da zabe a kasa.

Ya kuma kara da cewa, Katin zabe fiye 94,766 na nan a ofishinsu masu shi basu zo sun karba ba, saboda haka ya bukaci jamiyyun siyasa da sauran hukumomin gwamnati su taimaka wajen fadakar da jama’a bukatar su zo su karbi katin zabensu.

Da yake jawabi a waje taron, shugaban kungiyar kiritoci ta kasa (CAN) reshen jihar Adamawa Bishop Stephen Dami Mamza,ya nuna damuwarsa a kan yadda aka nuna wa ;yan guidun hijira da sansanin ‘yangudun hijira na karamar hukumar Michika, ya ce, babban abin takaici ne hukumar ta ce ba zata iya gudanar ya ragistan masu kada kuri’a ba a yankin saboda tsaro.

Exit mobile version