Hukumar kula da jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta Nijeriya (JAMB) ta sake dawo da jarabawar auna fahimta wacce ake yi kafin shiga jami’o’i, inda da aka bayyana mafi karancin maki na shiga gurbin jami’o’i.
Mafi karancin maki da ake bukata dalibi ya ci kafin shiga jami’a shine maki 120, a yayin da maki 100 shine na makarantun kimiyya da fasaha da kwalejin ilimi, yayin da makarantun kirkira maki 110.
An sanar da hakan ne a zaman masu ruwa da tsaki da akayi da shugabannin jami’o’i, manyan kwaleji da makarantun kimiyyya a jiya Talata a Abuja.
Shugaban hukumar jarabawan Farfesa Ishaq Oloyede ne ya tabbatar da hakan inda yace, jami’o’i zasu fitarda sunan dalibai zabin farko a ranar 15 ga watan Oktoba, sai zabi na biyu kuma a ranar 15 ga watan Disamba, daga nan sauran daliban kuma zasu jira sunan su a jerin sunayen sauran makarantu.