Muazu Hardawa" />

Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Bauchi Ta Shirya Taron Bita Ga Masu Ruwa Da Tsaki

A ci gaba da gudanar da shirye shirye domin tafiya aikin Hajjin bana cikin nasara, hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar bauchi ta shirya taron bita wa masu ruwa da tsaki da kuma jagororin aikin Hajji da wasu maniyyata, inda aka ilmantar da su sanin makamar aiki na kwanaki uku domin samun nasarar gudanar da wannan aiki ba tare da wata matsala ba.

Taron wanda aka gudanar da shi a dakin taro na masallacin fadar mai martaba sarkin Bauchi  ya gudana a ranar juma’a zuwa lahadi, inda aka tara jami’an jin dadin alhazai na kananan hukumomi da malamai da masu taimakawa alhazai da sauran ma’aikatan hukumar  aka  gabatar da kasidu da suka shafi ingancin aikin ibadar Hajji a saukake tare da tattaunawa kan duk wata matsala da kuma samar da hanyar magance ta cikin sauki, da kuma amsa tambayoyi daga mahalarta taron.

Kwamishinan harkokin addinini na Jihar Bauchi Alhaji Ado Sarkin Aska shi ne ya wakilci gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar na Jihar Bauchi inda a cikin jawabinsa ya yi fatar alheri ga maniyyatan na bana tare da jan hankalin su wajen ganin sun bayar da wakilci na gari da zai kare martaba da sunan Nijeriya a kasa mai tsarki. Har wa yau ya shawarci mutanen da aka dora musu nauyin taimakawa mahajjatan da su yi aiki da hakuri da kuma gaskiya don ganin an taimakawa mutane kamar yadda gwamnati ke shirye wajen bayar da duk wani agaji da aka saba don samun nasarar gudanar da aikin hajjin na bana kamar yadda aka saba a sauran shekaru.

Dokta Baba Lawan na cikin wadanda suka gabatar da lacca a wajen taron inda ya shawarci jagororin alhazai da su ilmantar da su muhimmancin rike guziri da kuma lura da dokokin kasar Saudi Arabia inda ya bayyana cewa guziri shi ne babban al’amari ga mahajjaci saboda samun ingancin ibada cikin natsuwa. Don haka ana bayar da kudi cikin dalar Amurka 800 don haka mutane su rike su da muhimmanci saboda su takwas ake bayarwa kuma idan mutum ya sake ya yi asarar guda daya zai fiskanci wahala sosai. Haka kuma ya bukace su da a koyar da mahajjata muhimmancin rike katin shaida da agogon hannu da ake basu wanda ke nuna inda mutum ya fito da kuma matsayin sa na alhaji don a gujewa shiga cikin matsala a yayin gudanar da aikin Hajji.

Shi ma Alhaji Mohammed Gadauji Turakin Katagum Mamba a cikin hukumar aikin Hajji ta Jihar Bauchi cikin jawabin sa ya ja hankalin mahajjata da su inganta niyyar su game da wannan ibada tare kuma da kiyaye dokokin kasa da kasa don a samu nasarar aikin da aka sa a gaba. Don haka ya shawarci jagororin da ke tallafawa alhazai da su gudanar da ayyukan su bil hakki da gaskiya ba tare da yin abin da za a samu bata suna ko korafi daga mahajjata ba.

Shi ma Sakataren  mulki na hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar Bauchi Alhaji Alkasin Danlami Shall cikin jawabin sa ya ja hankalin maniyyata da su rika daukar darasin da ake karantar da su game da yadda ayyukan za su gudana cikin sauki da nasara. Don haka ya ja hankalin su kan su dauki guziri a matsayin al’aura wajen kiyaye shi, saboda idan mutum ya sake guzurin sa ya salwanta zai yi rudewar da za ta iya shafar ayyukan sa na Hajji saboda a halin da ake ciki kudin guziri da takardun shaida na tafiya sune manyan abubuwan da ake mayar da hankali kan su don a samu ingantuwar ayyuka a lokacin aikin Hajji kuma idan mutum ya rasa wani daga cikin su zai wahalar da kansa ya kuma wahalar da jami’an gwamnatin da ke aiki domin lura da shi saboda samun nasarar wannan aiki.

Sakataren hukumar Alhazai ta Jihar Bauchi  Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa, cikin hirar sa da wakilin mu ya bayyana cewa a bara gwamnan Jihar Bauchi ya biya kudin tallafi na naira dubu 85 ga kowane Alhaji don a tabbatar da samun ci gaba da zama a masaukan su da ke kusa da Harami don su rika fita zuwa sallah a kan lokaci su dawo gida duk lokacin da suke so. Don haka a bana gwamnan ya ci gaba da bayar da tallafi don Alhazan su ci gaba da zama a wannan masauki da suka zauna bara. Sabanin wasu jihohi da suka rika komawa nesa da harami don a samu ragi daga kudin da suke biya.

Hakan ya jawo mutanen da suka biya kudin ajiya na naira milyan daya da rabi a bana an samu saukin ragi na fiye da naira dubu 23 wanda za a mai da wa mutanen da suka biya wannan adadi, don haka kowa yana iya zuwa inda ya biya wannan kudi don ya karbi sauran rarar kudin sa.

Bayan haka Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa ya ja hankalin mutanen da suka biya kudi a bara aka samu rara ba su zo sun karbi kudin su ba da su hamzarta zuwa da fasfunan da suka je aikin hajji da su domin su karbi sauran rarar kudin su, idan ba haka ba kuma za su mayar da wannan kudi zuwa hukumar aikin Hajji ta kasa da ke Abuja idan mutum ya zo daga baya kuma sai ya je can ya karbi rarar kudin sa.

 

Exit mobile version