Daga Idris Aliyu Daudawa,
Hukumar kula da farashin albarkatun mai ta kasa (DPR) ta bayyana cewa tana tilasta sayar da litar man fetur kan Naira 162 da kuma Naira 165, a matsayin farashin litar mai a Jihar Anambra. Okiemute Akpomudjere, jami’in kula da ayyuka na Hukumar, a Ofishin Awka, shi ne wanda ya bayyana hakan, a wata hirar da ya yi da manema labarai a Abuja ranar Juma’a.
Akpomudjere wanda ya yi wannan maganar ne ta hannun manajan shi na ayyuka, Bictor Ojiakor, ya ce hukumar ta sa ido ne tun ranar Litinin don tabbatar da komawa zuwa farashin da ake sayar da man. Ya dage kan cewa ba a kara farashin albarkatun man fetur ba. Akpomudjere ya nuna gamsuwarsa da dillalan man fetur a Jihar kan gyara famfunan da suke yi zuwa farashin na hukumar.
Ya ci gaba da karin bayani ‘Yan kasuwa a Awka a ranar 12 ga Maris, sun kara farashi daga Naira175 zuwa Naira 212, wannan kuma ya biyo bayan jita-jitar da aka yi ta yadawa, game da farashin mai da Hukumar kayyade farashin albarkatun mai tayi (PPRA). “Shugabannin mu sun ba da umarnin cewa mu tabbatar da cewa‘ yan kasuwar sun sayar a kan Naira 162 da kuma Naira165, kuma a matsayin mu na ofis mun matsa don tilasta hakan.