Connect with us

KIWON LAFIYA

Hukumar Kiwon Lafiya Ta duniya Ta Yi Gargadi Kan Tarin Fuka

Published

on

Duk da yake cewar majalisar dinkin duniya ta ja kunnen al’umma cewar ba kamar yadda ake tsammani ba, mutane kalilan ne za su mutum a sanadiyar cutar tarin fuka daga shekarar 2017, akwai bukatar kasashe su kara daukar matakai saboda a kawo karshen ita cutar nan da shekar ta 2030.

Hukumar ta bayyana cewar duk da yake ana daukar matakai dagha matakin kasashen duniya,  hakan ya yi maganin mutuwar mutane milyan 54 a sanadiyar cutar tarin fuka, har yanzu ita ce babbar cutar da take da illa a duniya.

Hukumar lafiya ta duniya a rahoton ta na ranar Fuka ta duniya ta wannan shekara wanda aka fitar ranar Litinin, ya yi kira da a kara mai da hankali na kasashen duniya gaba daya.

Shi yasa tayi kira ga shugabannin kasashe hamsin da kuma shugabannin siyasa wadanda za su taru a majalisar dinkin duniya, a karo na farko saboda taro akan cutar tarin fuka, su dauki matakin daya dace, wahjen yin amfani da matakan da shugabannin kasashen Indiya, Rasha Ruwanda da kuma Afirka ta Kudu.

Da yake bayani akan bukatar daukar matakin daya kamata a dauka saboda kawo karshen cutar, babban jami’in na majalisar dinkin duniya Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewar Bamu taba ganin irin wannan taron ba wanda aka ba muhimmanci da kuma fahimtar juna, akan bukatar shugabannin duniya su kawo karshen cutar tarin fuka, sai mu yi amfrani da ita wannan damar, mu yi wani abu saboda kawo karshen wannan babbar annoba.

“Saboda a samu cimma burin kasashen duniya wanda tsaikon da ake so ke nan saboda kawo karshen cutar tarin fuka nan da shekara ta 2030, kkasashe ya dace su kara zageb damtsen su, saboda su kara taimakawar da suke yi gida da daji wajen ita yakar cutar”.

Shi ma a tashi gudunmawa akan tsare tsaren cutar tarin fuka Dokta Tereza Kaseba ya bayyana cewar, yadda ake samun mutwar milyoyin mutane, wanda kuma akwai magunguna amm sai idan an dauki matakai da sauri, ana iya yin maganin su cututtukan ko cutar da ake gani kamar bata da magani arkar da ita. “ Wannan b aba wani abin da za a amince da shi bane, cewar mutane da yawa wadanda suka kai milyoyi suna rasuwa, wasu kuma suna shan wahala kullun daga cutar da ake iya maganin ta.Muna bukatar mu hada karfi da karfe mu yi maganin wannan cutar, wadda take da babbar matsala ga walwala da kuma jin dadin wahala, wadanda ake bari wadanda wata damarsu akwai lokaci,tare da kuma wadanda ba a daukki cewar su wani abu bane, tare da kuma wadanda da kyar suke samun yadda za a kula da lafiyarsu, “wannan shi ne lokacin da za a dauki mataki”.

Hukumar lafiya ta duniyab ta bayyana cewar zata dauki wani mataki wanda zata yi amfani da hakan, saboda ta samu cimma wani buri, kamar wadnda suke dauke da cutar TB, ta hanyar bullo da wasu tsare tsaren saboda cimma burin cikakkiyar kulawa da lafiya.

Ita hukumar ta bayyana cewar matakan da zata dauka sun hada da hadin kai ta kungiyoyi masu zaman kansu, da kuma sauran wasu masu ruwa da tsaki, su hada karfi da karfe wajen kawo karshen babbar
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: