Connect with us

LABARAI

Hukumar Kula Da Aikin ‘Yan Sanda Ta Gaiyyaci Mutum 6,253 Don Daukarsu Aiki

Published

on

Hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta mika goron gayyata ga mutum 6, 253  da suka samu nasara don a fara horas dasu da kuma daukarsu aikin ‘yan sandan Nijeriya.

Sanarwar ta ce, wadanda aka mannan sunayensu a shafin intanet na hukumar ranar Asabar zasu wuce makarantar horas da ‘yansanda ranan ko kafin ranar 13 ga watan Yuni na wannan shekarar.

Sanarwar ta ce, “Ana shawartar dukkan wadanda suka samu nasara dasu duba sunayensu da inda aka turasu don ci gaba da samu horon a babban ofishin ‘yansanda na jihohinsu.

“Za a fara horaswar ne ranar Jumma’a 8 ga watan Yuni 2018, za kuma a rufe shiga makaratun gudanar da horon ne ranar 13 gawatan Yuni na 2018, duk wanda bai samu shiga makarantar horaswar zuwa ranar 13 ga waran Yuni 2018 ba, ya nuna kamar bai amince da daukakar da aka yi masa ba kenan.”

Hukumar ta ce, zata dauki sabbin ‘yan sanda har 6,000, amma bincike ya nuna cewa, wadanda suka samu nasara 6,253 ne zasu shiga shirin horaswar da za a gudanar.

Wakilinmu ya gano cewa, kowanne karamar hukuma nada mutum 7, yayin da aka rarraba saura guraben tsakin jihohi.

Jihar Kano ce keda mutum mafi yawa inda suke da wadanda suka samu nasara 308 daga nan sai jihar Katsina inda suke da mutum 238, a sunayen da aka fitar makon daya gabata sunayen mutum 5,107 aka ware don suyi gwajin asibiti don ci gaba da karbar horaswar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: