Hukumar kula da kasuwannin kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, adadin kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin ya zarce miliyan 57 ya zuwa karshen watan Maris, wanda ya kai kaso 92.3 bisa dari na jimillar baki daya. Kazalika, a rubu’i na farko, adadin sabbin kamfanoni masu zaman kansu da aka kafa a kasar ya kai miliyan 1.979, wato karuwar kashi 7.1 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, kuma ya zarce matsakaicin ci gaban da aka samu a shekaru ukun da suka gabata. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya)