Hukumar Kurkukun Kuje Ta Saka Takunkumin Hana Sanatoci Ganin Ndume

Na'urar

Daga Rabiu Ali Indabawa

An hana wasu sanatoci damar ganin Sanata Ali Ndume a gidan gyaran yalin Kuje da ke Abuja.

An garkame Ndume ne a maimakon Maina, tsohon shugaban kwamitin hukumar kula da farfado da fansho, bayan da ya tsaya ma sa a matsayin mai amsar belinsa, inda shi kuma ya yi batan dabo tun bayan hakan.

Sanata Na’Allah, wanda ya je ganin sa, ya ce, bai taba ganin irin wannan wulakancin ba. An dai hana sanatoci damar ganin Ndume ne bisa sanya takunkumi daga hukumar gidan yarin da ke Kuje a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

An garkame shi ne a ranar Litinin, saboda rashin samun damar bayyana tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, wanda ya tsaya wa. Alkali Okon Abang na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya umarci a damke Ndume bayan wanda ya tsaya wa ya kasa bayyana a kotu a kan zargin badakalar Naira biliyan 2 na kudin fansho, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Masu rajin kare hakkin bil’adama suna bukatar a saki Ndume iya wuya. Duk da bayanai sun kammala a kan yadda aka ga sanatoci suna kai-kawo a gidan gyaran hali don ganin Ndume a ranar Talata.

Sanata Ishaku Elisha Abbo, sanatan PDP na Adamawa, inda aka ji yana ce wa Sanata Bala Ibn Na’Allah, na APC jihar Kebbi, ya tambayi ma’aikatan gidan gyaran hali a kan su bari a ganshi, amma sam sun hana shi ganinsa. Sai da sanata Na’Allah suka tattauna da Abbo tukunna aka basu damar shiga wani ofishi.

An ga sanatan ya shiga ofishin wani babban jami’i, G. U. Ochepa, bayan ya cika dokokin kariya daga Korona. An ji Ochepa yana ce wa sanatan: “An hana ziyara saboda Korona, hakan ba horo ne ga sanatan ba.” Lauyansa da matansa ne kadai za su samu damar ganinsa. Bayan ya yi mintoci 20 a ofishin Ochepa, sanatan ya bar gidan gyaran halin. Na’Allah ya nuna tsananin tsoron da ya shiga a kan kama Ndume da aka yi.

“Tsawon shekaru na a matsayina na lauya, wannan ne karo na farko da naga irin wannan wulakancin. Na san in dai har tsayayye ya kasa bayyanar da wanda ya tsaya ma wa, kudi zai biya na beli. “Kudin belin ne ya kamata ya biya, amma ban taba ganin an garkame tsayayye ba a maimakon wanda ya tsaya wa,” a cewarsa.

A jiya mun ji cewa Sanata Ali Ndume, wanda ma’aikatan gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, suka tafi da shi a ranar Litinin, a bisa umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja, zai daukaka kara a kan hukunci da aka yi masa yau, Talata. Lauyan Ndume, Marcel Oru, ya ce za su daukaka karar ne yau a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja, kamar yadda Daily Trust ta tabbatar. A cewarsa, ba a bai wa Ndume damar jin ta bakinsa ba, sannan ba su bashi wasu takardu da ya bukata ba don ya kare kansa.

A wani ci gaban labarin kuma, Aliyu Maina, dan uwan Abdulrasheed Maina, ya roki kawunsa a kan ya mika kansa ga ‘yan sanda. Maina na fuskantar shari’a a kan almubazaranci da kudaden fansho.  An tsare Sanata Aliyu Ndume wanda ya tsaya wa Maina a matsayin jingina a gidan maza, a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba Kwanaki biyu bayan babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tsare sanata mai wakiltan Borno ta Kudu, Ali Ndume a gidadan yari kan rashin gabatar da Abdulrasheed Maina a kotu, dan uwan tsohon Shugaban hukumar ta fansho, Aliyu Maina ya yi martani.

Aliyu ya bukaci kawun nasa a kan ya gabatar da kansa ga rundunar ‘yan sanda. Jaridar Banguard ta ruwaito cewa Aliyu ya ce, sake bayyanar Maina zai dakatar da tozarcin da Ndume ke fuskanta a idon duniya kafin lamarin ya tabarbare.

Majiyarmu ta tattaro cewa Aliyu, dan uwan Maina da kut-da-kut, ya ce sanata Ndume ya azabtu sosai a kan Maina. Ya kara da cewa abun bakin ciki ne ganin cewa yana biyan bashi don kawai ya taimaki dan mazabarsa. Aliyu ya yi kira ga Maina a kan ya taimaka ya dubi halin da ake ciki, cewa tserewar na kara tabarbarewar shari’arsa ne, sannan cewa ya gabatar da kansa don a samu damar kawo karshen al’amarin. Ya ce: “Na yi magana da Sanata Ndume da wasu hadimansa lokuta da dama kuma na basu tabbacin cewa Maina zai gurfana a gaban kotu da zarar ya warke, amma abin bakin ciki, ya ki aikata hakan. Ban sanya idanu a kansa ba tsawon watanni uku yanzu domin yana gudun kowa.”

Exit mobile version