Hukumar Kwastam Ta Kwace Wasu Motocin Alfarma Guda 12

PIC 18. OYO/OSUN AREA COMPTROLLER, NIGERIAN CUSTOMS SERVICES, ALHAJI MOHAMMED MUNDU SHOWING ITEMS SEIZED IN AIYEGUN BORDER OYO STATE ON MONDAY (5/9/11).

Hukumar kwastam ta tarayyar Nijeriya, wacce ta ke yankin “C” da ke garin Owerri, ta bayyana kwace wasu manyan motoci na alfarma guda 12, da kuma wasu kayan da akayi fasa kwaurinsu, kimar kudin fito na wadannan motoci da kayan da hukumar shelantawa kwacewa a cikin mako guda guda ya kai Naira miliyan 240.

Shugaban rundunar kwastam, Kayode Olusemire,  na yankin “C” ne ya bayyana hakan a ofishin shi da ke garin Benin, a daidai lokacin da ya nuna wa manema labarai motocin da kayan fasa kwaurin, dukkan kayan an kwace su ne a kusa da garin Benin.

An kama mutum uku da ake zargin suna da hannu wajen shigo da kayan fasa kwaurin, a yanzu haka suna taimaka wa jami’an kwastam din da muhimman bayanai, inda hukumar ta ke son jin wadanda suka mallaki wadannan kaya da a kayi fasa kwauri.

Motocin da kayan sun hada da, trakta kirar Iveco kimar kudin fiton ta Naira miliyan 4.05, ta na dauke da buhuna 633 na shinkafar ketare wanda kimar kudin fiton ta ya kai Naira miliyan 16.20, sai kulaye na abin shan “Lucozade Boost wanda kimar kudin shi ta kai Naira miliyan 1.82, dukkan adadin kudin fito kayan ya kama Naira miliyan 22.08 kenan.

Sai kuma mota kirar Toyota Venza 2013, wanda kimar kudinta ya kai Naira miliyan 12.91, sai marsandi kirar GLK 350 da kirar ML 350, wanda kimar kudinsu ya kai Naira miliyan 12.59 da kuma Naira miliyan 5.82, sauran motocin dukka na alfarma ne kirar marsandi, jimular kimar kudaden fiton su ya kai Naira Miliyan 130.

 

Exit mobile version