Daga Khalid Idris Doya,
Hukumar kwastam ta kasa wato Kwastam (NCS) ta bayyana cewa, ta tara harajin da ya kai Naira tiriliyan daya da rabi (N1.5 Trillion) a shekarar 2020.
Jami’in yada labarai na Hukumar, Joseph Attah, ne ya fadi hakan a cikin sanarwar day a rabawa manema labarai ranar Laraba a Abuja.
Mista Attah ya shaida cewar adadin kudin da ya zarce N1,380,765,353,462.00 ne suka samar a shekarar da ta shude, tare da tara kudin da ya zarce N1,342,006,918,504.55 a 2019 duk da annobar Korona da aka fuskanta.
Ali ya ce baya ga aikin samar da kudin harajin wanda ake kara samun cigaba a duk shekara, sun kuma kara inganta tsare-tsaren da zai baiwa jami’ansu damar fafada hanyoyin samar da kudin shiga wa kasa ta hanyar gudanar da nagartattun ayyuka.
“Mun kuma tsaya kai da fata kan tilasta bin ka’idojin biyan haraji daga ‘yan kasuwa ta hanyar tsarin kai tsaye na hukumar kwastam, ta haka ne muka samu nasarar kawar da tsohon tsarin da ke kawo tsaiko ko rashin bada damar ingancin na amfani da hannu “manual”.
“Sauran matakan sun hada da kara kyautata hanyoyin fadakar da masu ruwa da tsaki wanda ta hakan an samu karin samun jama’an da suke bin dokoki da kansu tare kuma da kara baiwa jami’anmu karsashin maida muradin kasa fiye da tasu ta kashin kai.”
Shugaban ya kara da cewa, rufe iyakokin kasa da aka yi a watannin baya, ya bada damar dole masu son shigo da kaya ta hanyoyin da suka dace biyan haraji yadda doka ta tanadar.
“Kafin dokar rufe iyakoki a ranar 20 ga watan Agustan 2019, harajin da ake iya samu ya kasance tsakanin biliyan hudu zuwa biliyan biyar, amma yanzu NCS ta na samar da haraji a tsakanin biliyan biyar zuwa tara a kowace rana.
“Tsarin Diflomasiyya yayin kullen iyakoki ya haifar da da mai ido sosai, ciki har da bada damar bin cikakken tsarin ECOWAS kan sufuri da gudanarwar hadin guiwa na sintiri a iyakoki.
“Ana bukatar hukumomi suke raba bayanan sirri domin tabbatar da dakile safaran kayayyakin da ba su dace ba ta barauniyar hanya daga makwaftan kasashe,” inji Hameed Ali.
Ya kuma shaida cewar sun samar da na’urorin da suke taimaka musu wajen samun bayanan sirri da kuma taimaka wa jami’ansu ta hanyar gano masu kokarin fasa gwabri da kuma wadanda ke shigo da kaya ta barauniyar hanya.
Ya nemi masu ruwa da tsaki da suke baiwa hukumarsu hadin kai domin cimma nasarorin da suka sanya a gaba.