Na'ima Abubakar" />

Hukumar Kwastan A Kano Da Jigawa Ta Tara Harajin Naira Biliyon 4.3 A Shekara

Daga Na’ima Abubakar, Kano

Babban Kwamandan hukumar Kwastan mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Alhaji Abbas Kasim, ya bayyana cewa hukumarsa ta samu nasarar tattara harajin da ya haura Naira Biliyon 4.3 tsakanin watan Janairun shekarar da ta gabata zuwa watan March na wanann shekara.

Kwanturolan ya na wannan jawabi ne ga manema labarai a Kano ranar Juma’ar da ta gabata kamar yadda hukumar ta saba gudanarwa a duk kashin farko na kowacce shekara.

Abba Kasim ya bayyana cewa abinda Hukumar sa ta samu bana ya haura abinda aka sa ran samu na Naira Biliyon 3.6 da Naira Miliyon 609.1, ya ce, an bamu umarnin tattara Naira Biliyon 3.6 a kashin farkon shekarar data gabata, amma  muka samu nasarar  tattara Naira Biliyon 4.3.

Hakazalika hukumar ta Kwastan mai kula da Jihohin Kano da Jigawa ta samu Nasarar kwace wasu nau’in kayan da aka haramta shigo kasar nan dasu  guda 41 wanda aka kiyasta kudin fitonsu ya tasamma Naira Miliyon 170.

Abubuwan da aka kwace sun hada da Shinkafa, Man girki, Taliya, Makaroni Sugar, Kayan Gwanjo da motocin takumbo.

Haka kuma kwanturolan Hukumar Kwastan din mai kula da Kano da Jigawa Abbas Kasim ya bayyana nasarar kame wasu kayan daban ranar Lahadi 1 ga Afril, 2018, na wasu nau’inkayan da aka hana shigowa dasu a Jihohin Kano da Jigawa. Kayan sun hada da buhu 500 na shinkafa wanda a ka yi satar shigar dasu cikin wake tare da dila 20 na kayan kwanjo da aka karbe a Kano.

Wasu daga cikin kayan an Kama su ne a  Kauyen Katankara dake  kan iyakar Maigatari da Kasar Nijar,  har yanzu muna ta kokarin kiyasta adadin kudaden fiton kayan da aka samu nasarar damkewa.

Haka kuma hukumar ta Kwastan ta samu nasarar damke wasu mutane hudu da ake zargi suna da alaka da kayan da aka kame, amma yace ana nan ana ci gaba da gudanar da bincike domin kaiwa ga sauran masu hannu a cikin wannan mummunar ta’ada, inji Abba Kasim.

Exit mobile version