Hukumar Kwastan Ta Kama Bindigogi Fiye Da Dubu Daya A Lagos

Hukumar hana fasa kauri ta Nijeriya, kwastam, mai kula da shiyyar tashar jiragen ruwa ta Tincan Island da ke a Legas, ta kama manyan bindigogi sama da dubu daya.

Shugaban hukumar kwastom na kasa kanar Hamid Ali mai ritaya, shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a yau Litinin. Shugaban Ya kara da cewa an shigo da bindigogin ne daga kasar Turkiya.

Bindigogin sama da 1,000 dai kamar yadda shugaban hukumar kwastom ya nuna, ko wacce daya tana iya hallaka mutane da dama a cikin lokaci guda. Ba kamar sauran bindigogi. Hukumar ta gano cewa bindigogin ana yi musu dure ne da harsashi — to sai dai ya ce hadarinsu ba ya misaltuwa.

 

Exit mobile version