Daga Umar Faruk,
Hukumar Kwaston ta Nijeriya ta gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Birnin-Kebbi karkashin Mai Shari’a Sunday Bassey Onu a jiya bisa sauraron karar da mahaifin Marigayi Abdulrahman Sani Bunza ya shigar kan zargin daya daga cikin jami’an hukumar ta Kwastom da harbe masa damsa har lahira a ranar 10 ga Nuwanba, 2020, a kusa da garin Filgila dake yankin Karamar hukumar Dandi a Jihar Kebbi.
Sai dai a zaman kotun a jiya, Lauyan dake tsaya wa wadanda ake kara, Barista Amina Kaoje, ta gabatar da korafinta cewa, an kai wa hukumar Kwastom takardar sammacin sauraron karar da aka sanya ranar 8 ga Maris, 2021, amma ba a ba su takardun abinda ake karar su a kai ba.
Ta kara da cewa, tun da yanzu ga ta a gaban kotun, tana neman kotun da daga sauraron karar har zuwa ranar 19 ga Maris, 2021, wanda zai ba su damar nazarin takardun karar da abubuwan ake zargin su da aikatawa, don maido da amsa ta hanyar sanya nasu takardu gaban kotun.
Shi ma lauyan mai kara, Barista Aminu Umar Kalgo, ya bayyana wa kotun cewa, “na yi mamaki idan lauyar hukumar Kwastom za ta bayyana wa kotun da cewa ba a ba su takardun karar ba, domin aikin rijistara ne ta bayyana wa kotu ko an kai wa hukumar Kwastom takardun karar da na sauraron kara ko ba a kai ba.”
Bisa ga hakan ya ce, “ba mu da wata jayayya game da rokon a dage sauraron karar har zuwa ranar 19 ga Maris, 2021.”
Lauyar hukumar Kwastom ta kara da bayyana kotun da cewa, “bisa ga yarjejeniya da amince a tsakaninta da abokin aiki, wato lauyan dake gabatar da karar, cewa, sun amince da aka dage sauraron karar har zuwa ranar 19 ga Maris, 2021, amma idan kotun ta amince da hakan, tana da damar sauraron karar a ranar da suke nema.”
A nata bangare, kotun a karkashin jagorancin Mai Shari’a Onu ya ce, kotu za ta shiga hutu a cikin kwanan. Saboda hakan zama bada lokacin da ya dace da za a dawo, don sauraren karar.
Don haka kotun ta daga sauraren karar har zuwa 16 ga Afirilu, 2021, don dawowa a cigaba da sauraren karar.
Wadanda ake karar dai sun hada da Hukumar Kwastom da shugabanta na kasa bisa zargin halaka wani matashi da jami’in hukumar ya aikata a shekarar bara.