Daga Abubakar Abba
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta bayyana ƙudirinta na yin aiki da masu ruwa da tsaki kafaɗa don sake gina cibiyoyin lafiya dake ynkin Gabas Maso Yamma da yaƙin ‘yan Boko Haram suka ɗai-ɗaita.
Daraktan Hukumar na Yankin Afirka, Dakta Matshidiso Moeti ce ta sanar da hakan a taron manema labarai a Maiduguri Babban Birnin jihar ta Borno.
Matshidiso ta ce, lokaci ya yi da za a kawo wa cibiyoyin lafiyar dake jihar waɗanda yaƙin ya ɗai-ɗaita.
Daraktan wanda ta ƙaddamar da gangamin yaki da cutar shan Inna da cutar cizon Sauro ya ce, Hukumar, ta jima tana bada taimako wajen bada magungunan cututtukan musamman yaki da cututtuka shida da suke saurin hallaka yara ƙanana a yankin.
A cewar ta,“muna bada taimako wajen ciyar da tsare-tsare na yaki da cutar ta cizon Sauro da kuma kawo ɗauki waɗanda suka haɗa da bada shawarwari ta ƙwararru ga zaukacin matakan gwamnatin jihohi da na tarayya.
Ta ci gaba da cewa; “mun bada taimako akan ɗaukacin matakan lafiya, musamman lokacin bada agaji na gaggawa don tabbatar da cewa, mutane sun samu kular data dace.”
Daraktan ta ce, “ mun janyo tawagar masu taimakawa wajen harkar Lafiya har 130 da za a tura su yankin don taikamawa gwamnatin Jihar ta Borno akan fannin lafiya.”
Tayi nuni da cewar, ganin yadda yaƙin ke zuwa ƙarshe a yankin, akwai buƙata ta gaggawa don a kawo canjin, don tabbatar da an ƙyra kayan
kula da lafiyar da yaƙin ya ɗai-ɗaita. Tace, Hukumar tare da haɗin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki akan harkar lafiya, sune ke kan gaba wajen ganin an sake gyara kayan na aikin lafiya.
A ƙarshe Moeti ta ce; “ganin cewar yaƙin yanzu ya lafa, muna sa ran sauran masu ruwa da tsaki akan harkar lafiya da su ɗauki nauyin sake gyara kayan aikin lafiyar, musamman gabin alumomin dake yankin da suka yi gudun hijira, sun fara komawa gidajensu, ita kuma gwamnatin jihar, ta ɗauki nauyin sake gyara matakan lafiya na farko na jihar.