Abubakar Abba" />

Hukumar Masana Magunguna Ta Kulle Dakunan Ajiye Magunguna 378 A Osun

Hukumar magunguna ta kasa (PCN) ta kullle dakunan ayiye magunguna guda 378 da kuma kulle kemis  20 a jahar Osun a bisa kin bin ka’idojin da hukumar ta gindaya masu na rabar da magunguna da adana su.Daraktar sanya ido da dubwa na hukumar uwargida Antonia Aruya ta shaidawa manema labarai hakan a garin  Osogbo bayan da hukumar ta aaiwatar da matakin a a cikin satin da ya gabata. Antonia Aruya  ta kuma koka akan yawan karuwar ‘yan kemis a kafada a jahar likiticin kafada wadanda kuma basu da wani ilimi da kuma karuwar masu kemis barkatai a jahar. A cewar Aruya bai kamata a bar marasa ilimi suna sayar da magunguna ba domin za su iya jefa lafiyar alumma a cikin hadari, inda ta jadda da cewar, dole ne ko wannne shagunan sayar da magaungun su yi rijista da hukumar don a samu a ci gaba da basu lasisin rabar da magunguna. Daraktar ta bayyana cewar,  ya zuwa yau hukumar ta kai ziyara ga jahohi ashirin da bakwai dake cikin kasar nan kuma hukumar ta gano cewar a cikin jahar Osun suna sayar da magunguna ba tare da bin ka’ida ba kuma sauran basu da wani ilimin sayar da magunguna.

Ta yi nuni da cewar, abin takaici asu masu sayar da magunguna  a jahar ko turaci basa ji kuma suna sayar da magunguna ta haramtacciyar hanya, inda hakan yake jefa lafiyar alumma a cikin hatsari.  A cewar ta, wannan zuwan na hukumar jahar shine na biyu, musamman ganin yadda masu sayar da magungunan suke nuna kunnen kashi na kin bin dokokin da hukumar ta shin fida na sayar da magunguna da kuma rabar dasu. Tace, “ mun kai ziyara sassa da dama na jahar tun a ranar litinin, inda a karshen aikin mun kai ziyara ga jimmalr harabar kamafanonin sarrafa magunguna guda  501  harda shaguna. A cewar ta an baiuwa harabobin sarrafa magunguna tara umarnin subi ka’ida kula da magunguna su yadda ya kama akan laifuffukan da suka tabka da suka hada da rashin kula da magungunan su yadda ya dace da rashin tsafta da tattara magungunan da sauran su. Aruya ta shawarci alumma dasu tabbatar da sun sayi magungunan da aka yi masu rijista don kaucewa sayen maguungunan da za su jefa lafiyar su a cikin matsala. A karshe ta ce, hukumar ta samar da tsari na yin sana’ar musamman don samar da magunguna masu inganci da kuma rabar dasu.

 

Exit mobile version