Connect with us

LABARAI

Hukumar NAHCON Ta Yi Zagayen Aiki A Rumfunan Mahajjatan Jihohi

Published

on

A shekaran jiya ne Hukumar Kula da Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta gudanar da wani kayataccen zagayen aiki a rumfunan mahajjatan jihohin Nijeriya.

Zagayen wanda aka kasa shi gida uku, wanda rukunin ‘A’ ta kasance tawagar da Shugaban Hukumar ta NAHCON, Barista Abdullahi Mukhtar ya jagoranta; sauran rukunan kuma su ne, rukunin ‘B’ da rukunin ‘C’. A cikin tawagar ta Shugaban NAHCON din akwai Ambasadan Nijeriya a Saudiyya, Mai Shari’a Abdullahi Dodo.

Tawagar ta shugaban hukumar na NAHCON ta fara ne da ziyarar rumfunan Mahajjatan Jihar Kano, inda aka saurari jawabi daga shugabannin tawagar mahajjatan da kuma wasu daga cikin mahajjatan.

A yayin jawabinsa, Shugaban Hukumar ta NAHCON, Barista Abdullahi Mukhtar ya taya mahajjatan murna da sauke farali, tare da fatan Allah ya amshi ibadunsu.

Ya ce; “Muna alfahari da abin da Jihar Kano ku ka yi. Za mu lura cewa, idan akwai wani alhajin Jihar Kano da bai je Madinah ba, sai dai wanda bai biyo jirgin Jihar Kano ba, amma duk wanda ya biyo jirgin jihar sai da ya shigo ta Madina.

“Zaman Mahajjatan Jihar Kano a Madina, Makkah zuwa Muna zuwa Muzdhalifa, Arfa da dawowa Muna mun shaidi yadda ku ka yi da’a, ku ka bi ka’idojin da aka shimfida na abubuwan da ake so da wadanda ba a so a aikata.

“Wani kyakkyawan misali a wannan shekarar shi ne yadda daukacin tawagar jagororin Jihar Kano suka zauna a rumfunan da mahajjata suke. Amirul Hajj, Sakataren hukuma jin dadin alhazai da sauransu duk suna rumfuna daya da mutanensu.” Inji shi.

Sakataren Kwamitin Zagayen rumfunan wanda Hukumar NAHCON ta yi, Ahmed Sani ya bayyana wannan ziyarar rumfuna a matsayin wani mataki na zagaye don gaisawa da mahajjatan Nijeriya, tare da yi musu ban gajiyan aikin Ibadan da suka gudanar.

Haka kuma Hukumar ta kara da cewa, wannan zagaye an saba shirya irinshi a kowacce shekara, bayan an kammala Arfah da kuma kwanakin karshe na zaman Muna. Daga cikin makasudin ziyarar akwai jin shawarwari daga shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na jihohi da kuma su kansu Mahajjatan. Haka kuma duk wanda ke da korafi akan wani lamari yana iya gabatarwa ga hukumar domin a magance.

A nasa jawabin Babban Sakataren Hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Danbatta ya jinjinawa Hukumar Kula da Alhazai ta kasa bisa irin namijin kokarin da ta yi wurin tabbatar da walwalar mahajjata tun daga zaman Muna, zuwa Arfah da dawowa Muna.

Daga cikin Mahajjatan Kano da aka saurari ra’ayoyinsu a yayin ziyarar akwai Rufa’I Abdullahi daga karamar hukumar Garko, wanda ya bayyan cewa; “Abin da ya ke bani sha’awa a matsayina na sabon Alhaji (wanda ya fara aikin hajji a karo na farko) abubuwan da wadanda suka zo a baya suka sanar da mu kafin zuwanmu, a zahirin gaskiya mun ga canji matuka. Tun daga Madina har zuwa Makkah da wannan muhalli na Muna. A Madina, abin gunin ban sha’awa, da zarar ka tsallake titi sai masallacin Annabi (SAW). Ba abin da za mu ce sai dai mu yi godiya ga Allah da hukumar Kula da Alhazai ta Nijeriya.”

Daga karshen ziyarar, Shugaban Hukumar ta NAHCON ya zagaya wurin da ake dafawa Mahajjatan abinci domin gane wa idanunsa yadda ake gudanar da madafar da irin abincin da ake dafa musu.

A wannan jerin ziyara, tawagar ta ziyarci sauran jihohin da suka hada da Kwara, Zamfara, Kaduna, Kogi, Katsina, Sakkwato da sauransu. Haka su ma sauran rukunan guda biyu sun ziyarci sauran jihohin Nijeriya kamar yadda aka tsara.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: