Abubakar Abba">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NOMA

Hukumar NALDA Za Ta Horar Da Matasa 400 A Gombe Don Noma Kadada 300 

by Abubakar Abba
December 22, 2020
in NOMA
2 min read
Hukumar NALDA
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Hukumar Aikin Noma ta (NALDA) ta sanar da cewa, za ta horas da matasa 400 a karkashin shirin bai wa matsa joron aikin noma na kasa na NYFW ta hanyar yin hadaka da kwalejin renon ‘ya’yan itatuwa ta kasa FCH da ke a Dadin Kowa a cikin jihar Gombe kuma ta bayar da kadada dari a matsayin hadaka.

Bugu da kari Hukumar ta ce, ta kuma fara shirin farfado da kadada 300 a jihar Gombe, inda ta kara da cewa, kadadar 300 da Hukumar ta NALDA ta ke da su, za sake farfado da su a bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

samndaads

Babban Sakataren Hukumar ta NALDA Prince Paul Ikonne wanda ya sanar da hakan, ya bayyana cewa, za a horas da matasan ne a fanin noman rani, ya ci gaba da cewa, Hukumar za ta kuma yi hadaka da ciyar domin kara samar da ayyukan yi ga matasan ta hanyar aikin noma domin wadata kasar da abinci.

Ikon ne wanda ya sanar da hakan a lokacin da ya kai ziyara a kwalejin ya ci gaba da cewa, kadadar dari, da kwalejin ta bayar, za ayi amfani da su ne domin noman rani, inda za a dauki matasa fiye da 400, inda Babban Sakataren Hukumar ta NALDA Prince Paul Ikonne ya ci gaba da cewa, dukjan kayan da aka yi watsi da su, za a sa ke farfado da su, inda ya kara da cewa, Hukumar ta NALDA na kuma son yin hadaka da gwamnatin jihar Gombe don a cimma bukatar shugaban kasa na wadata kasar da abinci.

Babban Sakataren Hukumar ta NALDA Prince Paul Ikonne ya bayyana cewa, Hukumar ta NALDA za ta fara maganar rattaba yarjejeniya da kwalejin za ta kuma samar da kudade a zaman wadanda za a fara yin amfani da su kan aikin, inda ya sanar da cewa,, Hukumar za ta kuma yi samar da fahimta a tsakanin juna.

A cewar Babban Sakataren Hukumar ta NALDA Prince Paul Ikonne, fannin aikin noma na daya daga cikin ajandar shugaba Buhari, inda ya samar da tsare-tsare don kara bunkasa aikin noma a daukacin fadin kasar da kuma samar da ayyukan yi ga matasa,

Babban Sakataren Hukumar ta NALDA Prince Paul ya jinjina wa shugaban kwalejib kan kafa hadakar da kuma samar da sauran ofis – ofis na hukumar, inda ya yi alkawawarin cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yin kokari domin farafado da aikin noma don amfabin ‘yan kasa baki daya.

Da ya ke yin tsokacin kokarin na Babban Sakataren Hukumar ta NALDA Prince Paul, Shugaban kwalejin Dakta Babawuro Mahmoud Ali, wanda Daraktan sashen gudanar da bincike na kwalejin Mallam Abubakar Haruna Sai’id ya wakilce shi ya ce, ziyarar ta Prince Paul ta na da kyau kuma ta zo a kan gaba, inda ya ci gaba da cewa, Allah ya albarkanci kwalejin da kasar noma mai kyau da kuma kwararrin jami’ai da fannin aikin noma na kasar ke bukata.

Daraktan ya ce, kwalejin a shirye ta ke ta yi hadaka da Humumar ta NALDA, inda ya kara da cewa,burin shugabannin Buhari shi ne, a kara samar da abinci a kasar da kuma kara samar da ayyukan yi ga matasa ta hanyar aikin noma.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kungiyar FOGAN Za Ta Dauki Matasa Miliyan Bakwai A Fannin Noma

Next Post

Kotu Ta Wanke Likitan Da Ake Zargi Da Kashe Maradona

RelatedPosts

Manoman Masara A Gombe Za Su Dara – Kwamishina 

Manoman Masara A Gombe Za Su Dara – Kwamishina 

by Abubakar Abba
21 hours ago
0

Kwamishinan Gona da Dabbobi na Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Magaji...

An Sharwaci Nijeriya Ta Rika Tattaunawa Da Masana’antun Madara Na Cikin Gida

An Sharwaci Nijeriya Ta Rika Tattaunawa Da Masana’antun Madara Na Cikin Gida

by Abubakar Abba
21 hours ago
0

Darakta Janar na kungiyar nan ta, wato NECA, Dakta Timothy...

Tanadin Abinci Yana Da Mahimmanci Ga Al’umman Nijeriya, Inji Ministan Noma

Akwai Wawaken Gibi A Bangaren Noman Zamani A Nijeriya, Cewar Nanono

by Abubakar Abba
21 hours ago
0

Ministan Ma’aikatar Aikin Noma da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono...

Next Post
Maradona

Kotu Ta Wanke Likitan Da Ake Zargi Da Kashe Maradona

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version