Muhammad Sani Chinade" />

Hukumar NDE Da NERI Sun Rarraba Kayayyakin Gudanar Da Sana’o’i Ga Mata 150 A Jihar Yobe

Hukumar Samar da aikin yi ta kasa NDE da taimakon hukumar dake kula da yankin jihohin area mask gabashin kasar nan dake fama da rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram NERI sun bada tallafi ga Matan da suka rasa mazajensu sanadiyyar rikin Boko Haram su kimanin 150 a Jihar Yobe.
Wadannan mata sun hada da Mayan dake dauke da cutar nan mai lakabi da kabari kusa HIb musamman Mayan da mazajensu suka rasu sanadiyar wannan cuta, kuma matan aksarinsu sun fito ne daga kananan hukumomin Yunusari da Gaidam.
An kaddamar da bada wannan tallafi ne na bada kayayyakin gudanar da sana’o’i Jim kadan da kammala horon da aka basu, da yake jawabi shugaban riko Na karamar hukumar Gaidam Wanda Daraktan kula da sha’anin mulki na karamar hukumar Modu Nanami, yace hukumar NERI ta Samar da aikin ya ga dubban mata a wannan yanki basu.
Don haka ya nuna matukar godiyarsu ga wadannan hukumomi dangane da kokarin da suke yi Na kawo daukinsu ga al’umma wannan lamari ne mai matukar muhimmanci.
A sakon ta ga wadannan mata da suka amfana da wannan tallafi Kodinetan hukumar Samar da aikin yi ta kasa NDE mai kula da JIhar ta Yobe Hajiya Mairo Aliyu Betara ta hori matan ne da suka ririta abubuwaan da aka basu son tsayawa da kafafuwansu.
Kodinetan ta kuma hori matan da su guji sayar da wdannan kayayyakin sana’o’i, su yi amfani da su tk hangar da aka horar da su musamman son taimakawa iyalensu.
Matan dai an horar da sune ta bangaren mabambanta sana’o’i da suka hada da dinki, yadda ake matsar mai, toya kosai da makamantansu.
Kayayyakin da aka rarraba musu sun hada da na’urar sanyaya ruwan sanyi refrigerator, kekunan dinki , buhunan masara, buhunan wake da buhunan gyada da manja da kuma injunan nika da sauransu.
Wassu daga cikin matan da suka amfana Hajja Kaka Lawan da Paulina Sunday godiyar suka mika a madadin dukkanin matan ga hukumomin NDE da NERI dangane wannan tallafi fa suka basu. Sun bada tabbacin yin amfani da kayayyakin ta hanyoyin fa suka dace don taimakawa iyalensu ba tare da sun sayar da su ba.

Exit mobile version