Daga Hussaini Yero,
Hukumar samar da ayyukan yi ta kasa (NDE) reshen Jihar Zamfara ta kaddamar da shirin koyawa matasa ayyukan yi na musamman, su 14,000 a fadin jihar. Darakta Janar na Hukumar na kasa Abubakar Nuhu Fikpo, shi ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin ranar Asabar din da ta gabata, a Gusau babban Birnin jihar.
A jawabin Daraktan, shirin zai fara tun watanni uku da suka gabata amma abin takaici ya yi jinkiri saboda wasu matsaloli, ya kasance an samu tsaikon kaddamar da shi. “A cewarsa, an tsara shirin koyar da ayyukan na musamman ne domin ceto rayuwar matasa 774, 000 marasa aikin yi na tsawon watanni uku masu zuwa.
Kazalika, a cikin adadin wadannan matasa 774,000 Jihar Zamfara matasa 14,000 za su amfana da shirin, wannan shirin zai lakume Naira miliyan 84. a tsawon wata uku kowane matashi zai amfana da Naira 60,000, ma’ana a kowane wata zai karbi alawus na Naira 20,000 a tsawon watanni uku.
Abdullahi Yakubu ya jinjinawa Hukumar NDE ta kasa wajen ganin ta dukufa wajen samar wa matasa aikin yi a fadin kasar, kuma wannan shirin yana taimakawa gaya wajen ceto rayukan matasa da dogaro da kansu. A karahe Ko’odinetan ya yi kira ga matasan da suka samu shiga cikin wannan shirin da su mai da hankali wajen ayyukan da za a koya masu.