Daga Rabiu Ali Indabawa
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wasu kwayoyi masu dauke da hodar Iblis, tabar wiwa da kuma wasu kwayoyi masu karfin gaske da aka yi jigilar su zuwa kasashen Ingila, Northern Ireland, Australia, Maldibes da New Zealand.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Mista Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a cikin wata sanarwa.
Babafemi ya ce an gano wani mashahurin mai fataucin, Mista Sikiru Owolabi, wanda daya ne daga cikin biyun da aka tsare an kama su bayan da jami’an na NDLEA suka sa ido sosai kan lamarin. A cewar sanarwar, wakilan masu safarar miyagun kwayoyi da ke hade da wasu kamfanonin aika sakonnin na duniya da ke Legas ne suka kame.
“Sikiru Owolabi, wanda ya yi bayani mai gamsarwa yayin bincike, an binciko kilogiram daya na hodar iblis da aka boye a cikin kwantenan man shafawa ‘Cream’ wanda akai nufin kai wa Dublin na Arewacin Ireland an kama shi a ofishin jakadancin a Legas. Wannan kuma ya biyo bayan gano wasu nau’ikan giram 200 na hodar iblis da aka yi niyyar shiga da su London da United Kingdom duk a cikin wannan tafiya. ”
A wani aikin sirri, an kama giram 320 na kwayar heroin da aka boye a cikin ‘yan kunnen da ke zuwa daga Congo zuwa Australia a wani kamfani da ke Lagas, kamar yadda aka kame wasu giram 390 na hodar iblis a cikin kayan maza su kuma za a kai zuwa Arewacin Ireland duk a kamfanin guda.
Kazalika an yi nasarar kama giram 500 na Satiba na wiwi da aka boye a cikin motocin da ke zuwa New Zealand a dayan kamfanonin jigilar kayayyaki, giram 200 na Methamphetamine da aka boye a jikin lambar yabo don zuwa New Zealand, tare da wasu giram 200 na methamphetamine da aka boye a cikin wani littafi su kuma za a kai zuwa Maldibes, an kama su daidai a cikin wani kamfanin na daban.
NDLEA ta ce baya ga kamun Owolabi, ana ci gaba da bin diddigi tare da cafke sauran masu fataucin a bayan sauran haramtattun kwayoyi wadanda ba sa tare da su wadanda aka hada su a matsayin kayan fataucin zuwa Turai.
Shugaban kuma babban jami’in Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, wanda ya yaba wa maza da jami’ai da ke cikin ayyukan, ya ce “Ina rokon dukkan mazajenmu da jami’anmu da ke cikin ayyukan boye da sarari a duk fadin kasar don ci gaba daukar wadannan matakai har sai mun kori masu laifin da abubuwa da suke yi nan haramtacciyar kasuwa.”