Sulaiman Ibrahim" />

Hukumar NDLEA Ta Kama Buhun Tabar Wiwi 34 A Gwagwalada

Tabar Wiwi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), reshen yankin Gwagwalada da ke Abuja, ta cafke buhunan tabar wiwi 34.

Shugaban NDLEA, Kwamandan FCT, Mista Lawan Hamisu, ya tabbatar da kamewa da kuma kama wani da ake zargi ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba a Abuja.
Hamisu ya ce an kamasu ne da sanyin safiyar ranar Talata, 29 ga Disamba, ya kara da cewa an shigo da kayayyakin ne a cikin wata babbar motar wani kamfanin (wanda aka sakaya sunanshi).

Kwamandan ya fadawa NAN cewa aikin yana daga cikin sintiri na musamman na karshen shekarar da hukumar ke yi domin dakile haramtattun magunguna da ake safarar su a cikin kasar nan.
A cewarsa, an kama wani mutum da ake zargi, Mohammed Abdulganiyu, dan shekara 35, wanda yake tuka babbar motar, a kan hanyar Okene, Kogi zuwa Kano.

Ya ce wanda ake zargin, a lokacin da jami’an NDLEA ke yi masa tambayoyi, ya ce bai taba shiga cikin harkar haramtattun kwayoyi ba.
Abdulganiyu ya roki hukumar ta NDLEA da ta yi masa sassauci.

Kwamandan, yayin da yake yabawa jami’ansa da suka cafke wanda ake zargin, ya bayyana kamen a matsayin babbar nasarace wajen daukar kyakkyawan mataki na kawar da muggan kwayoyi daga yaduwa.
“Har ila yau, muna ci gaba da gudanar da ayyukanmu, a kan babbar hanyar Lokoja, Abuja da kuma Kaduna.” Inji kwamandan.

Exit mobile version