Hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) ta fara raba kayan agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Shugaban hukumar, ABM Mohammed Muhammad, wanda Mr Imam Garki, ya wakilta ya ce, kayayyakin da aka fara raba wa sun hada da kayan abinci da kayan gini da kuma kayan amfanin yau da kullum.
Ya ce, raba kayan ya zama dole don rage wa al’umma matsalolin da suka shiga sakamakon barnar da ambaliyar ta yi musu.
“A halin yanzu muna cigaba da raba irin wannan kayan a kananan hukumomin Chikun da Kaduna ta Yamma muna fatan kai agajin ne ga akalla gidaje fiye da 838,” inji shi.
Ya kuma shawarce su da su tabbatar da sun yi amfani da kayyakin yadda yakamata don rage radadin da suke fuskanta.