Connect with us

LABARAI

Hukumar Nema Ta Tallafa Wa Wadanda Ta’addanci Ya Shafa A Karamar Hukumar Dandume

Published

on

Hukumar NEMA a karkashin Gwamnatin tarayya ta baiwa Gwamnatin jihar Katsina buhunan kayan abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum domin raba wa kananan hukumomin da ta’addanci ya shafa domin tausaya masu. A cikin kananan hukumomin akwai karamar hukumar Dandume ta sami buhuna sama da 2000 na abinci buhunan sun hada da buhunan Shinkafa da Masara da na wake dukkansu masu nauyin kilo biyu da rabi da kuma sauran kayan amfanin gida irinsu jarkokin man girki guda 70 da bargunan rufa da katifun kwanciya da gidajen maganin sauro da shaddoji da katan-katan na magi.

A lokacin da yake jawabi wajen kaddamar da kayayyakin a sakatariyar karamar hukumar Shugaban riko na karamar hukumar Alhaji Ahmed Idris Mashi ya ce, wannan kayan milyoyin Naira da karamar hukumar ta samu ya zo ne daga Gwamnatin tarayya tare da kokarin gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagorancin gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari Dallatun Katsina don a tallafa wa wadanda ta’addanci ya shafa a karamar hukumar ba wai an biya su bane a’a don a tausaya masu kuma a kara nuna masu lalle Gwamnati ta damu kuma Gwamnati ta dauki mataki don kawo karshen dukkan ta’addanci a karamar hukumar da jihar Katsina da ma sauran jihohin arewacin kasar nan.

Alhaji Ahmed Idris ya ci, gaba da cewar a karamar hukumar akwai mazabu guda 5 da ta’addancin ya shafa mazabun sune akwai Magaji Wando, da Jiruwa, Dantankari A, da Dandume, da mazabar Dantankari B, ya ce, dukkan wadannan mazabu akwai sunayen wadanda abin ya shafa da kuma adadin da kowa zai samu, ya ce, tuni Gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagorancin Kwamishinan wasanni da Matasa Alhaji Danladi Katsina ta kafa kwamitocin da za su raba kayan a kowacce mazaba akwai kwamiti na mutum 10,  kwamitin ya kunshi Maigarin Garin wanda shi ne zai jagoranci kwamitin akwai shugabar mata da shugaban Jam’iyyar APC na mazabar da shugaban Matasa da dai sauran ‘yan kwamitin wanda yawansu ya kai goma.

Shugaban riko na karamar hukumar ya yi kira ga ‘yan kwamitin su ji tsoron Allah kuma gobe Allah zai tambayesu kuma karamar hukuma ma ba za ta yarda ba duk wanda aka kama da aikata rashin gaskiya wajen rabon kayan za su hukunta shi kamin aje lahira inda Allah zai tambayesu saboda amana ce aka basu, ya ce mutane su shaida kwamitin karamar hukumar ma sun sauke nauyinsu kuma Allah ya gani yadda suka yi, kuma ya yi kira ga mutanen da za su amfana da wannan kayan kyauta ne kada wanda ya bada ko kwabo. ya gode ma Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari da hukumar NEMA da gwamnatin jihar Katsina ya ce, babu shakka Gwamnan jihar mutum ne mai tausayi da son ganin karshen ta’addanci a jihar kuma mutane su tashi tsaye da addu’oin samun zaman lafiya,  mutane su gyara halayensu, Sakataren kwamitin na karamar hukumar Shugaban jin dadi da walwala na karamar hukumar Alhaji Kabir Inuwa Faskari ya karanta jadawalin yadda za’a raba kayan da yawan mutanen da ta’addancin ya shafa a kowacce mazaba.
Advertisement

labarai