Hukumar noma ta NIRSAL ya bayyana cewa, ya samar da sama da naira biliyan 148 a shelkarar da ta gabata, domin zuba su a matsayin kudin jari a kan harkar yin noma domin riba a kasar nan.
Manajin Darakta na kamfanin Abdulhameed ya sanar da hakan, inda ya ci gaba da cewa, ayyukan da kamfanin ya gudanar a cikin watanni sha uku da suka wuce, sun kai sama da 3,000, muamman wadanda aka gudanar a tsakanin kungiyoyin manoma da suka kai har gfuda 500,000, inda manoma suka noma kadada kusan 800,000.
A cewar Manajin Darakta na kamfanin Abdulhameed, a cikin watannin sha uku an samar da ayyukan yin nomad a suka kai na sama da naira biliyan 30 tare da kuma samo kudade daga gun bankunna dake kasar nan da kuma sauran wasu hanyoyin samar da kudade.
Manajin Darakta na kamfanin Abdulhameed ya ci gaba da cewa, koda yake an samu raguwar ayyukan na noma saboda kakaba dokar hana zirga-zirga da aka yi a daukacin fadin kasar na bayan bullar annobar Korona a kasar nan shekarar 2020.
Sai dai, Manajin Darakta na kamfanin Abdulhameed ya bayyana cewa, saboda zurfin ilimin da muke da shi na fasahar zamani kan harkar aikin noma, hakan ya samar mana da mafita.
Manajin Darakta na kamfanin Abdulhameed ya ci gaba da cewa, “Kamar yadda ku sani ne, ya zama wabi a ci gaba da yin kari da kuma samar da kayan aikin yi, musamman domin a samu nasarra yakara annonar ta Korona a kasar nan iadan aka yi la’akari da irin dimbin koma bayan da ta haifar wa fannin na aikin noma a Nijeriya”.
Manajin Darakta na kamfanin Abdulhameed ya kuma bayyana cewa, “A zaman mu na wadanda suka yi fice a harkar yin noma don riba a kasar nan, har yanzu kofarmu a bude take ga wadanda gwamnatin tarayya ta bai wa dama su zagaya cikin fadin kasar nan domin samar da wadataccen abinci a daukacin fadin kasar nan”.
A cewar Manajin Darakta na kamfanin Abdulhameed, kamfanin ya kuma samar da dimbin ci gaba a kasar kan kan fannin na noma domin riba, inda hakan ya bai wa kamfanin damar zuba sama da naira biliyan148 a matsayin jari a fannin na yin noma don riba a zango na hudu na shekarar 202o da ta wuce.
Manajin Darakta na kamfanin Abdulhameed ya kara da cewa, an kuma dora kimanin mutane miliyan 1.4 a cikin shirin Inshora da kamfanin ya kirkiro da shi wanda kuma aka gudanar da shi a karkashin yin hadaka.