Connect with us

LABARAI

Hukumar NIS Ta Dakatar Da Bada Takardar Izinin Shiga Kasa Kai Tsaye Ga Bakin Da Suke Shigowa Nijeriya

Published

on

Hukumar shigi da fici ta kasa, NIS, ta dakatar da bayar da takardar shaidar shiga cikin kasar nan kai tsaye ga dukkanin bakin da ke shigowa har sai hali ya yi.

Binciken da wakilinmu ya yi a ranar Talata a Filin sauka da tashin manyan Jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas, ya gano cewa a yanzun hukumar tana bayar da takardar izinin bizan shiga kasa ne kawai kamar yadda aka saba ga bakin da suke shigowa cikin kasar nan.

Wata tabbatacciyar majiya ta shaida mana cewa, a ranar 12 ga watan Yuni ne aka kaddamar da bayar da takardar izinin ta kai tsaye ga bakin na kasar nan a kan dala 110, amma sai aka kuma dakatar da bayar da ita bayan kwana guda da fara yin aikin da ita, kan muhawarar da ake yi na kudin da ake biyan.

A cewar majiyar tamu, an dakatar da bayarwan ne a bisa umurnin babban kwanturolan hukumar na kasa, Muhammad Babandede, domin a sami warware matsalar biyan kudaden.

Majiyar ta ce, “Sam ba gaskiya ne ba, cewa hukumar tamu tana karban kudaden daga bakin na kasar nan domin ta ba su bizar ta kai tsaye.

“Kudaden bizar kai tsayen hukumar, ‘Online Integrated Serbices (OIS) da New Works, ke karban su ta yanar izo, wadanda ma’aikatar cikin gida ta sanya yin wannan aikin.

“Ita Online Integrated Serbices (OIS), tana karban dala 90 ne, ita kuma, New Works, tana karban dala 20 domin bayar da bizar. Ana kuma iya biyan kudin ta yanar gizo ne tun ma kafin a shigo cikin kasar nan, ko kuma a biya da katin biyan kudi in an shigo.

Sai dai kuma, koke ya yawaita daga wasu mutanan da ke cewa suna biyan kudin kafin su iso Nijeriya, sannan kuma in sun iso sai a bukaci da su sake biyan kudin.

“Hakan ne ya sanya babban Kwanturolan ya yi umurni da a dakatar da bayar da bizan, sai hali ya yi.

Majiyar ta ce, manyan kasashen duniya kamar Amerika, Ingila China, Afrika ta kudu, duk suna bayar da bizar ta kai tsaye ga bakin na su.

“Wannan fa hanya ce mai kyau mai kuma sauki. A maimakon a ce sai mai son zuwa kasar nan daga waje ya je neman bizan a ofishin jakadancin kasar nan da ke can kasar na su, sai kawai ya aiko da bukatar na shi ga hukumar namu, ya kuma hado da fasfo din shi da dukkanin takardun da ake nema na dalilin zuwansa, da inda za shi a cikin kasar da makamantan hakan.

“Matukar ya cika sharuddan ya kuma hado har da tikitin Jirginsa na komawa shikenan.

 

Advertisement

labarai