Hukumar NIS Ta Kafa Tarihin Samar Da Manhajar Horaswa Ga Jami’anta

Jami’an hukumar shigi da fice na kasa (Nigeria Immigration Service), 68 ne suka halarci wani taron horaswa na musamman domin kara fahimtar makaman aiki dai-dai da manhajar horaswa na tsawon wata guda a Kwalejin koyon aikin hukumar da ke Sakkwato. Shirin da aka gudanar da shi wanda zai kara haskakawa da ilmantar da jami’an hukumar sabbin dabarun aiwatar da ayyukan nasu, ya zo ne dab da lokacin da hukumar ke shirin gabatar da bukin cikar ta shekaru 55 da kafuwa a watan Agusta mai zuwa.Shugaban hukumar na kasa, Muhammad Babandede MFR da mataimakin sa kan tsare-tsaren horas da Jami’an duk sun halarci wajen bukin rufewan wanda aka yi ranar Laraba a kwalejin jami’an hukumar da ke Sakkwato.A jawabin da ya yi wajen taron, Babban Kwanturolan hukumar, Muhammad Babandede MFR, ya nu na matukar jin dadin sa ne ga wadanda suka yi tunanin tsara wannan mahimmin shirin, suka kuma nu na hanyar da ya kamata a bi wajen aiwatar da shi. Inda ya nu na cewa, a ranar ne za a baiwa wadanda suka halarci kwas din takardun shaida, yana cewa, “Darussan da ku ka karba daga wadannan fitattu kuma zababbun manyan Farfesoshin sannan kuma kwararru a fannonin su, hakan ya ba ku daman kasancewa fitattu a tsakanin tsararrakin ku.“Domin ba abu ne mai sauki ba, a iya tara fitattun Farfesoshi har 23 tare da makusantar su 6 a waje guda, amma abin alfahari ne tara wadannan manyan Maluma waje guda da masu Kaki! Sannan kuma ba ma taron na su ba kadai, sun ma gabatar da zafafan makalolin su masu cike da ilimi, kwarewa da darussa. Wannan wani abu ne da ya kamata dukkanin sassan tsaro (Sojoji, da sauran sassan tsaro) su yi koyi da wannan muhimmin taron. Ina kara mika godiya ta musamman ga Farfesa Ingawa, wanda ya yi matukar kokari wajen hada wannan gadar ta zama a tsakanin masu sanye da Kaki da kuma manyan Farfesoshi Malaman Jami’a.“Ina alfaharin sanar da ku cewa, wannan shine karo na farko da hukumar shige da fice ta samar da manhajar horaswa ga jami’anta, tun daga lokacin da aka kafa ta a shekarar 1963. Ina da kuma tabbacin wannan sabon abin da aka kirkiro zai samar da kwararrun Jami’ai da za su sake fasalin hukumar tamu da nufin kara mata inganci. Ina son na kara tunatar da dukkanin Jami’an hukumar tamu cewa, ‘Komai inganci da kyawun

kayan aiki, matukar babu kwarewar masu amfani da kayan aikin, tamkar akwai da babu ne.’

“Manyan cibiyoyin namu da suka sami wannan garabasar halartan wannan atisayen su ne: Command & Staff College Sokoto. Nigeria Immigration Training School, Kano (ITSK), Nigeria Immigration Training School, Orlu, Nigeria Immigration Training School, Ahoada.
“Na jima tun daga lokacin da na shiga wannan aikin ina buri a cikin zuciya ta, na ga an samar da horon da ya dace da zamani, sahihi mai inganci, inda za a horas da Jami’anmu a kuma
karfafa masu gwiwa kan aikin na su. To kuwa matakin da aka cimma wa a wannan kwas dinyana gaskata mafarkin nan ne da na jima ina yin sa.“A nan ina kara yin jinjina ga Farfesa Salihu Ingawa, da tawagarsa ta manyan kwararru, Farfesoshi, Likitoci da sauran zababbu a kan fannoninsu, wadanda baccin kasantuwar su a wannan wajen ba,
ba ta yadda za a iya samun nasarar
wannan kwas din mai cike da abin
tarihi.
“Ina kuma yin wata jinjinar ta musamman ga manyan jami’an

hukumar tamu karkashin jagorancin
Mataimaki na, ACG Musa Madu, ina farin cikin shaida maku, tabbas kun
bayar da naku gudummawar kun
kuma rubuta sunayen ku a kundin
tarihin wannan hukumar namu.
“Ina kuma ba dukkanin
kwararrun da suka halarci wannan
kwas din tabbacin, za a dabbaka
dukkanin abubuwan da ku ka
karantar ba tare da wani bata lokaci
ba. mun kuma ba ku damar ci gaba
da duba ko mun aiwatar da koyarwar
naku yanda ya kamata.
“Na kuma yarda da gaskiyan da
aka fada na cewa, samar da yanayin
da za a yi aiki wanda ya dace, yana
da mahimmanci wajen kaiwa ga
manufofin wannan kwas din. don
haka ina ba ku tabbacin dukkanin
bukatun da shugaban wannan
makaranta ya bayar da kuma duk
shawarwarin da sauran kwararru
suka bayar a jiya, za mu kula da su
sosai daidai gwargwadon karfin da
kasafin kudin da aka yanka mana
ya bamu”. Kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana.
A na shi jawabin, Kwamanda ACG
Musa Madu, ya fara ne da yin godiya ga babban Kwanturolan hukumar
da tawagar sa, da kuma dukkanin
kwararrun da suka halarci bikin baiwa
Jami’an hukumar takardun shaida
bayan karewar kwas din. sannan ya
yi nu ni da irin jimiri da hazakan da
manyan Farfesoshi 30 da da suka
halarci kwas din wadanda aka gayyato
su daga manyan cibiyoyin hukmar
gami da Shalkwatar hukumar ta kasa
suka nu na, inda ya ce, sun rika yin
aiki ne dare da rana, har da ranakun
hutu na Asabar da Lahadi, wanda
hakan ne ya kai ga cimma nasarar da
kwas din ya samu.
“Yana mai nu ni ga Babban
Kwanturolan hukumar na kasa da
cewa, “Ranka shi dade, tun da dai kai
da kanka ne ka kirkiro wannan kwas
din mai dimbin mahimmanci, to ya
kamata ka adana tare da tabbatar
da aiwatar da darussan da aka koya
a cikin sa. Wanda sakamakon hakan
shi ne tabbatuwan mafarkin nan
naka, na samun nagartattun Jami’ai,
kwararru a wannan hukuma tamu.
“A nan kuma ina son na kara
tunatar da babban Kwanturola
shawarin da kwamitin hadin gwiwa
na wannan taron ya bayar game da,
kayan aiki, kyautata yanayi mai kyau,
wajen bayar da horo a wannan cibiya
tamu. Musamman ina yin karin tuni
kan kudaden alawus din malamai da
karin girma a duk lokacin da hakan ya
dace, muna bayar da shawarar a fifita
wannan bangaren.
“A na su bangaren, kwararrun sun
bayar da shawarar da a fara aiwatar da
darussan da aka koya ba tare da bata
lokaci ba, a dukkanin cibiyoyinmu
guda hudu, a daidai lokacin da a
yanzun haka darussan da aka koyan
suke sabbi a kirazan jami’an da suka
halarci kwas din.
“kwararrun sun kuma bayyana
aniyar su na sadaukar da lokutan
su inda suka kasa kansu Manyan
malamai biyu da kuma Jami’inmu
guda da nufin ziyartar kowacce daga
cikin cibiyoyin namu domin su ga irin
ci gaban da aka samu a sakamakon
wannan kwas din da suka yi.
“A karshe ina kara nanata cewa,
wannan shi ne babban kwas mai tarin
ilmantarwa da jami’anmu da suka
halarta suka samu, wanda zai ba su
daman fahimtar duk inda suka dosa a
wannan aikin na su”, in ji ACG Madu.
Wannan sabon yunkuri na
inganta ayyukan hukumar da
shugabanta Muhammad Babandede
ke yi ya zo dai-dai da kudirin
gwamnati mai ci a yanzu ta Shugaba
Muhammadu Buhari da ta yi
alkawarin kawo sauyi mai ma’ana ga al’ummar Nijeriya.

Exit mobile version