Connect with us

RAHOTANNI

Hukumar NIS Ta Nuna Takaicin Yadda Matafiya Ke Bijire Wa Dokar Shige Da Fice

Published

on

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta nuna takaicinta da irin yadda wasu matafiya da ke shigowa kasar nan suke bijire wa tsarin tantancewa na shige da fice bayan sun dawo tafiya daga kasar waje.
Mai rikon mukamin jami’in yada labarai na hukumar, Mista Amos Okpu ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a madadin shugaban hukumar, Alhaji Muhammad Babandede a jiya Juma’a.
Amos Okpu ya nunar da cewa irin wannan mummunar dabi’ar ta fi aukuwa ce a manyan filayen jiragen sama na kasar nan.
Ya kara da cewa, bijire wa tsarin tantance masu shigowa cikin kasa ya saba wa ka’idar tabbatar da tsaro a filin jirgin sama da kan iyakar kasa. “Irin wannan dabi’ar ta saba wa sashe na 15, karamin sashe na 1 zuwa na uku na dokar shige da ficen kasa ta shekarar 2015”, in ji shi. Sanarwar ta cigaba da cewa, “Wannan sashen da sauransu, yana bukatar dukkan fasinjojin da suke shigo cikin kasa ko fita su garzaya zuwa wurin jami’in shige da fice domin tantance su. A bisa hakan, dukkan fasinjoji ciki har da ‘Yan Nijeriya da ke fita waje ko dawowa daga waje walau ta jirgin sama, ko jirgin ruwa ko ta kan-tudu su bi ka’idar dokar kamar haka: Su bi ta kofar da aka amince a shigo ko fita ta cikinta tare da gabatar da kansu ga jami’in shige da fice domin tantancewa.
“Su kuma kasance suna da takardar fasfon tafiye-tafiye zuwa waje ko kuma takardar shaidar Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), idan sun kasance ‘yan asalin daya daga cikin kasashen kungiyar. Haka mutum ya kasance yana da takardar izinin shiga kasa ta Nijeriya ko kuma ta kasar da yake son zuwa”.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: