Muhammad Sani Chinade" />

Hukumar SEMA Ta Yobe ta tallafa Wa Mutum 20,000 Da Abinci

Hukumar kai daukin gaggawa (SEMA) ta Jihar Yobe ta kaddamar da aikin ba da tallafin gaggawa na kayayyakin abinci ga mutane kimanin dubu 20 da ke cikin matsanancin hali a fadin Jihar musamman ga wadanda suka hadu da iftila’in barnar ruwan sama da makamantan haka.

Tun kafin wannan lokaci dai hukumar ta SEMA sai da horar da wasu jami’an ‘yan sa kai su kimanin 178 don gudanar da wannan aiki Na rarraba kayayyakin tallafi a dukkan fadin jihar.

Da yake jawabi ga wakilinmu bayan kaddamar da wannan shiri babban sakataren hukumar ta SEMA a jihar, Dafta Mohammed Goje, sun shiga wannan shirin ne ganin cewar fiye da Rabin yankunan jihar sun fuskanci wannan iftila’i.

Don haka ne y kirayi al’ummomin da za su amfana da wannan tallafi da su yi amfani da kayayyakin da aka ba su ta hanyoyin da suka dace kana su kum ci gaba da addu’ar fatan alheri ga wannan gwamnati taai Mala Buni bisa yadda ta kudiri aniyar cigar da jihar Yobe gaba.

Babban sakataren ya kara da cewar, wannan tallafi da yardar Allah zai kai ga dukkanin gundumomin jihar 178 wadda mutane kusan dubu 20 da suka yi fama da mabambanta matsaloli zasu amfana.

Ya ci gaba da cewar, gwamna ya samar da wadannan kayayyakin tallafi ne cikin lokaci don samarwa al’ummomin saukin rayuwa tare da basu kulawa ta musamman.

A cewarsa wannan tallafi wata hobbasa ne aka yi cikin lokaci kasancewar mafi yawa al’ummomin ba su kai ga girbe amfanin gonar su ba.

Exit mobile version