Hukumar kula da shari’a ta jihar Kano ta dauki matakin ladabtarwa a kan wasu jami’an kotuna hudu, inda ta dakatar da wasu magatakarda biyu tare da yin gargadi ga alkalan kotun shari’a biyu bisa nuna rashin kwarewa da cin zarafin aikinsu.
Mai magana da yawun hukumar, Baba Ibrahim ne ya fitar da sanarwar daukar hukuncin ladabtarwar.
- Ƴansanda Sun Damke Ango Da Abokansa Bayan Mutuwar Amarya A Jigawa
- Liverpool Sun Zama Zakaran Gasar Premier Bayan Lallasa Tottenham
Ibrahim ya bayyana cewa, an cimma matsayar ne a yayin taron hukumar karo na 80 da aka gudanar a ranar 22 ga Afrilu, 2025, bisa ga shawarwarin kwamitin korafe-korafen jama’a na bangaren shari’a.
Daga cikin wadanda aka dakatar har da Ibrahim Adamu, babban magatakarda na biyu a babbar kotun shari’a, wanda aka dakatar da shi ba tare da biyansa albashi ba na tsawon watanni shida.
Har ila yau, an dage kara masa girma bayan da aka same shi da laifin zagi da kuma yunkurin kai wa nagaba da shi hari – wanda ya saba wa dokokin ma’aikatan jihar Kano (2004) da kuma dokokin hukumar kula da harkokin shari’a.
A wata shari’ar kuma, Maigida Lawan, babban magatakarda na kotun daukaka kara ta Shari’a, an hukunta shi ne bisa laifin nema tare da kuma yunkurin biyan bukatun kansa ta hanyar da bata dace ba – karya.
Hukumar ta rage masa girma daga mataki na 13 zuwa mataki na 12 sannan ta dakatar da shi ba tare da biyansa albashi ba na tsawon watanni shida, nan take.
Har ila yau, Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci, Alkali Mansur Ibrahim, ya samu gargadi a hukumance bayan da aka tabbatar da cewa ya yi kalaman batanci ga mai kara.
An kuma gargadi abokin aikin sa Alkali Nasiru Ahmad, biyo bayan nuna bangaranci a shari’ar da ya yi.
Hukumar ta sake jaddada matsayar ta na yaki da cin hanci da rashawa da rashin da’a, inda ta yi gargadin cewa, duk wani jami’in kotu da aka samu da aikata rashin da’a zai fuskanci hukuncin ritayar dole.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp