Connect with us

LABARAI

Hukumar Shige Da Fice Ta Jinjina Wa Nasarar Da Nijeriya Ke Samu A Duniya

Published

on

Da yake al’ummar kasar nan suna bikin ranar dimukuradiyya a yau, inda a bana aka yi waiwaye a kan shekaru biyar na mulkin gwamnatin Shugaba Buhari, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa a karkashin shugabancin CGI Muhammad Babandede, ta nuna farin cikinta a kan irin gagarumar nasarar da Nijeriya ke samu wadda hukumar take taka muhimmiyar rawa a kai ta hanyar kaddamar da garambawul a fannin inganta matakan biza da hanyoyin bayarwa, al’amarin da ya taimaka wa saukaka wa bakin waje su rika shigowa Nijeriya domin gudanar da harkokin kasuwanci.

Nijeriya tana kara samun kima da daraja ta yadda ta cilla sama zuwa mataki na 39 a cikin jerin kasashen da aka fi saukaka hada-hadar kasuwanci a duniya a bisa sikelin saukaka hada-hadar kasuwanci na Bankin Duniya, sannan da sanya sunanta har sau biyu a cikin sahun kasashe 10 da suka fi samun habakar tattalin arziki.

Shugaban NIS, Muhammad Babandede

Har ila yau, hukumar ta kuma bayyana cewa, “mun yi la’akari da cewa har yanzu akwai jan aiki a gaba amma NIS ta dukufa ka’in-da-na’in wajen yin aiki tare da dukkanin matakan gwamnati don samun nasarar kawar da abubuwan da ke kawo tarnaki ga samun ci gaba domin tabbatar da cewa Nijeriya ta zama wuri mafi dadin gudanar da hada-hadar kasuwanci”.
Advertisement

labarai