Daga Mahdi M. Muhammad,
Hukumar SON a ranar Juma’a ta lalata tayoyi marasa kyau, siminti da wayoyi masu darajar Naira Miliyan 8.7 a Kaduna.
Kazeem Muhammed-Yahya, Shugaban gudanarwa ta hukumar SON din ne ya bayyana hakan yayin lalata kayayyakin a yankin Gonin Gora da ke kaduna.
“Abin da kuka gani a yau wasu kayayyaki ne marasa inganci wadanda aka kwace sakamakon aikin binciken kasuwarmu. Buhunan simintin da aka lalata wadanda suka kare ne amma ‘yan kasuwa suka sake cika buhunan. Tayoyi abubuwa ne masu hatsari a rai wadanda kan iya haifar da mutuwa da raunuka idan sun lalace”, in ji shi.
Ya lissafa kayayyakin da aka kwace tare da lalata su, sun hada da guda 370 na tayoyi marasa kyau wadanda suka kai naira miliyan 4.7, buhun siminti 134 da kudinsu ya kai naira miliyan daya da kuma wayoyi 307 na zamani wadanda basu da inganci.
Ya bayyana cewa, dukkannin kayayyakin da aka kamasu an yi masu gwaji don gano ingancinsu kafin lalata su.
Ya kara da cewa, aungiyar ta damu matuka game da cire kayayyaki marasa inganci daga kasuwa don ceton rayuka, fiye da gurfanar da wadanda suka saba doka.