Daga Hussaini Baba, Gusau
Hukumar Tsaftace Muhali a Jihar Zamfara ta yinkuro wajan samar da hanyoyin tara kudin shiga ga jihar. Mai ba wa Gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar shawara a hukumar, Honarabul Ibrahim Magaji Alja ne ya bayyana haka a lokacin da yake jagorantar aikin gangami na tsaftace magudanun ruwa a Gusau babban birnin jihar.
Honarabul Ibrahim Alja ya bayyana cewa, “Hukumar ta kammala shirinta tsab don ganin jihar ta amfana da ayyukan hukumar wajen inganta tattalin arzikin jihar, don haka ta bollo da shirin gayyato kamfanoni masu zaman kansu don samar wa al’umma jihar akwatin zuba shara a gidajen da ma’aikatu sannan a rinka biyan kamfanonin, su kuma kamfanonin na biyan haraji ga gwamnati”. Tare da cewa, “Ta irin wadannan hanyoyyin ne kasashe da dama suka cigaba. Samar da wadannan hanyoyin hakan zai kara bunkasa tattalin arzikin Jihar Zamfara gwargwadon hali”.
Kazalika, a cewar Hon Ibrahim ka yanzu hukumar ta kashe kudade masu yawa wajen aiwatar da aikin yashe magudanun ruwa da kwalbatoci da ma fitar da wasu hanyoyin ruwa don kauce wa hadarin ambaliya da hasarar rayuka da gidaje a fadin jihar.
A karshe, Hon. Ibrahim ya nuna takaicinsa ga wadanda ba su amfani da abubuwan zuba shara a unguwanni sai su rinka zubawa a a magudanan ruwa duk da kuwa akwai shi a unguwanniin. Ya ce wannan cutar da kai ne da kuma al’umma. Daga nan sai ya yi kira ga al’ummar jihar tasu da taimaka wajen bai wa wannan hukumar hadin kai don ganin an samu ingantatcciyar rayuwa, da kuma bai wa gwamnatin Abdul’aziz Yari hadin kai da adduo’i don ganin kudirinta ya hakaku na cigaban al’ummar wannan Jihar.