Hukumar UBEC Za Ta Gudanar Da Ayyuka A Makarantu 31 Domin Inganta Ilimi A Kaduna

el-Rufai

Hukumar bayar da ilimin bai daya ta kasa (UBEC) za ta dauki nauyin gudanar da ayyuka a makarantu 31 da ke cikin Jihar Kaduna, karkashin shirin kwaminin inganta ilimi ta shekarar 2019. Shugabar shirin inganta ilimi na hukumar UBEC reshen Jihar Kaduna, Misis Esther Jibji ita ce ta bayyana hakan a ranar Litinin a garin Kaduna a wajen taron kwana daya na masu ruwa da tsaki kan yadda za a aiwatar da shirin inganta ilimi na shekarar 2019. Jibji ta bayyana cewa, shirin inganta ilimi wanda hukumar UBEC ta samar da shi wani mataki ne na bunkasa makarantun gwamnati musamman ma a yankunan karkara da al’umma burane marasa galihu. Ta kara da cewa, hukumar SUBEB za ta dauki nauyin ayyukan kashi 90, yayin da al’ummar da za su amfana da wannan ayyuka za su dauki nauyin biyan kashi 10.
“Za a kwashe tsawan wata shiga ana gudanar da ayyukan na musamman, yayin da za a kammala kananan ayyuka a cikin watanni biyu.
“Makarantu za su gabatar da daftarin gudanar da ayyukan ga hukumar ilimi ta kananan hukumomi wanda ita kuma za ta mika shi zuwa hukumar SUBEB ta Jihar Kaduna, inda za ta lissafasu tare da mikasu ga hukumar UBEC ta kasa baki daya.
“Hukumar UBEC za ta bibiyi daftarin da SUBEB ta gabatar mata tare da zaban wadanda suka fi cancanta da shirin inganta ilimi kai tsaye.
“Hukumar UBEC za ta sanar wa makarantun da suka cancanta ta hannun SUBEB ta Jihar Kaduna,” in ji ta.
Jibji ta ci gaba da bayyana cewa, an gudanar da ayyuka guda 62 a shekarar 2018 wanda kudadansu ya kai na naira miliyan 31.5.
Da yake gabatar da jawabi, shugaban sashi na hukumar UBEC a yankin Arewa-maso-Yamma, Radiba Kagara ya bayyana cewa, an gudanar da taron ne domin samun fadakarwan da ake bukata wajen aiwatar da shirin a tsakanin masu ruwa da tsaki.
“Muna bukatar wakilan al’umma da masu ruwa da tsaki su san makasudin gudanar da aiki da sanin irin ayyukan da dubarun da za a zaba wajen gudanar da ayyukan.
“Wannan aiki yana jadda mahimmancin makaranta da kuma hanyoyin da al’umma za su shiga wajen bunkasa makarantu.
“Haka kuma, shiri ne na horarwa da samar da hanyoyin gabatar da dubaru na wasu ayyukan.
“Ina mai tabbacin cewa za a gudanar da cikakken shirin inganta ilimi na shekarar 2019 a garin Kaduna,” in ji Kagara.
Tun da farko dai, shugaban hukumar SUBEB na Jihar Kaduna, Mista Tijjani Abdullahi ya mika godiyarsa ga hukumar UBEC wajen inganta ilimi a cikin jihar. Abdullahi wanda ya samu wakilcin jami’in gudanarwa na hukumar, Dakta Christy Alademerin, ya bukaci masu gudanar da shirin inganta ilimi da su yi aiki kafada da kafada da dukkan sakateriyoyin ilimi na kananan hukumomin guda 23 da ke fadin jihar tare da tabbatar da ganin shirin ya samu nasara. Ya nuna goyan bayansa ga wannan shiri ga hukumar UBEC.

Exit mobile version