Connect with us

LABARAI

Hukumar UNICEF Da NOA Sun Shirya Taron Fadakarwa Kan Cutar Korona A Katsina

Published

on

Hukumar gyaran Akida ta kasa NOA reshen jihar Katsina tare da hukumar UNICEF sun shirya taron fadakar da kan shugabannin addinai da ma’aikatan hukumar gyaran Akida ta kasa NOA reshen kananan hukumomi 11 na shiyyar Funtuwa, a dakin taro na Otel din Elbintu dake Jabiri Funtuwa a jihar Katsina.
A lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron, Daraktar hukumar NOA na kasa reshen jihar Katsina Alhaji Armaya’u Liti Rimaye, ya yi kira ga Shuwagabannin Addini da su tashi tsaye wajen kara wayar da kan Mabiyansu a kan Cutar korona wadda take ci kamar wutar daji, kuma su bi ka’idojin da masana harkokin kiwon lafiya ke yi a kan illar cutar korona da yadda ake yada ta a tsakanin al’umma, ya zama wajibi mu kiyaye saboda cutar korona tana yaduwa ne ta hanyoyi da yawa.
Alhaji Armaya’u Rimaye ya ce, shi yasa hukumarsu ta NOA tare da Hukumar UNICEF suka hada gwiwa domin yakar wannan cuta ta hanyar kara ma juna ilimi inda hukumar ta gayyato Shugabannin Addinai kamar Shuwagabannin Addinin Musulunci dana Kiristoci tare da Ma’aikatansu na kananan hukumomin Funtuwa, Bakori, Faskari, dandume, Danja, Malumfashi, Sabuwa, kafur, Musawa da karamar hukumar Matazu don kara wayar da kan Shugabannin akan wannan cuta.
Daraktan ya ce, wasu ma basu yarda cewar akwai wannan cuta ba ko wasu suce wai cuta ce ta masu kudi ko ta jajayen Mutane da dai sauran jita-jita mara amfani don haka dole ne malamai su tashi tsaye wajen fadakar da Al’ummominsu musamman ta hanyoyin da ake kamuwa da wannan cuta kuma idan mutum yaji alamominta ya garzaya asibiti ko kuma mutum ya kira lambobin da hukumar NCDC ta bada a ko da yaushe.
Shugaban hukumar UNICEF a nashi jawabin yace cutar Cobid 19 ta shigo Duniya ne a cikin watan Disamba a shekarar da ta gabata watau a shekarar 2019 har yanzun cutar na yin illa ga jama’a kuma cutar ta shigo kasarmu Nigeriya a ranar 27 Fabarairu a shekarar 2020 kuma wani dan kasar Itali ya shigo da cutar Lagos, yaci gaba da bayyana hanyoyin da ake kamuwa da cutar cobid 19 kamar gaisawa da Jama’a da rashin sanya takunkumi na Fuska da yawan yin atishawa a cikin mutane ko kuma rashin sanya gwiwar hannu wajen yin atishawa da amfani da abin share majina na zamani da sauran hanyoyi da likitoci suka fadi domin yin amfani da su a matsayin kariya.
A Jawabin Limamin Masallacin Juma’a na Bakin Rawul Alhaji Abdulrahman yace Cuta gaskiya ce kuma suna fadakar da Jama’a a kan yadda za su kiyaye kansu wajen kamuwa da cutar korona da kuma shawarwarin da masana harkar kiwon lafiya suka bada. Daga karshe muna rokon Allah ya kiyaye mana wannan cuta da sauran cutututtuka, Amin.
Advertisement

labarai