Hukumar kula da aikin ‘yan sanda (PSC) ta amince da sallamar wasu manyan jami’an rundunar ‘yan sanda daga aiki. PSC ta sanar da cewa ta sallami jami’an daga aiki ne bayan samunsu da aikata laifuka daban-daban da suka sabawa aikin dan sanda.
Daga cikinsu akwai jami’an da aka samu da laifin safarar muggan makamai zuwa Nijeriya, da kuma rashin kwarewa a aiki.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da shugaban hukumar, Ikechukwu Ani, ya fitar tare da aika sako zuwa ga manema labarai a yau Lahadi. Mr Ani ya ce, hukumar ta dauki wannan mataki ne yayin wani zaman ganawa da hukumar ta yi ranar Juma’ar da ta gabata.
“An sallami babban Sufirtanda (CSP) na ‘yan sanda bisa rashin gaskiya da nuna halayen da suka saba da na jami’in tsaro. An sallami Sufirtanda (SP) bayan samunsa da laifin haɗa baki tare da wasu batagari domin sace na’urar rarraba hasken wutar lantarki a unguwa, wato taransifoma.”
Sai kuma karin wasu manyan jami’an guda biyu da suka hada da babban mataimakan sufirtanda (DSP) da mataimakin Sufirtanda (ASP), inji Ani.