A kokarin tabbatar da an yi wa kadarori rajisata, Hukumar yi wa kadarori rajisata karkashin dokar yi wa kadarori rajista ta shekarar 2017, wadda mukaddashin shugaban kasa, Farfeasa Yemi Osinbajo ya sa wa hannu,ta yi wa kadarori 20,684 wadanda kudinsu ya kai naira biliyan N392 rajista.
Gwamnan babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, ne ya bayyana haka a cikin mujallar Hukumar tare da kokarin da Hukumar ke yi na bayar da lamuni ga kanana da matsakaita da kuma manyan harkokin kasuwanci na haifar da da mai ido.
A ranar 24 Agusta, 2017 Hukumar ta yi wa cibiyoyin hada-hadar kudi 136 da bankunan ‘ya kasuwa 22 da bankunan al’umma 106 da wani bankin guda daya, da bankin da ke bayar da rance ga ‘yan kasuwa guda uku da wani bankin da ba ya karbar kudin ruwa da wasu cibiyoyin hada-hadar kudi , wadanda jimlarsu ta kai 16,236, rajista kuma an kiyasta kudinsu a kan naiara bilyan392. An sa ran Hukumar ta karfafa wa bankuna wajen amince da jigina wajen yin harka da bokan huldarsu. Haka kuma ana sa ran bankunan su rage karin kudin da suke yi daga kashi 75 ciikn dari zuwa kashi 53 cikin dari wajen karbar jinginar gidaje da filaye Bankunan kasuwanci ne suka fi yawan kadarori wadanda aka kiyasta kudinsu a kan naira biliyan 381, sai kuma wadansu cibiyoyin kudi guda uku da suk da kadarorin na naira biliyan10 . Haka kuma na sa ran Hukmar za ta taimaka wajen samar da ayyukan yi ta hanyar rage kudaden da ake karba in an karbi bashi.