Jagoran ‘yan adawa Raila Odinga, yayin shirin jawabi ga magoya bayansa a birnin Nairobi. Ranar 25 ga Oktoba, 2017.
Hukumar shirya zaɓen Kenya, ta dage shirin kaɗa ƙuri’u da yakamata a yi yau Asabar, a wasu yankunan da ‘yan adawa ke da rinjaye.
Hukumar ta ce, ta ɗauki matakin ne, don kaucewa sake samun zubda jini sakamakon arrangama tsakanin ‘yan adawar da jami’an tsaron ƙasar, zalika domin kare lafiyar jami’anta.
Rundunar ‘yan sandan ƙasar ta ce, akalla mutane 6 suka rasa rayukansu a dalilin rikici kan zaɓen shugabancin ƙasar da kotun koli ta bada umarnin sake wa, bayan soke na farko da shugaba mai ci Uhuru Kenyatta yayi nasara.
Karo na biyu kenan ana dage zaɓen a wasu manyan yankunan ƙasar guda hudu, lamarin da yasa ake zaman dar-dar, bayan kauracewa zaɓen da Odinga hadi da magoya bayansa suka yi.