Hukumar Zabe Ta Kasa Ta Sanar Wa Kotu Wajibcin Ta Na Yi Wa Dino Melaye Kiranye
Daga Wakilinmu
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, wato INEC, ta bukaci wani alkalin babban kotun tarayya da ke Abuja, wato Alkali Nnamdi Dimgba, da ya dakatar da umarnin kotun da ya hana hukumar ci gaba da batun yi wa Sanata Dino Melaye mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa kiranye. Kamar yadda hukumar ta shaida wa kotun, umarnin dakatar da ita daga ci gaba da shirin yi wa sanatan da lamarin ya shafa kiranye, an yi hakan ne ba tare da la’akari da abin da doka ta shimfida ba.
Mai shara’a John Tsoho na babbar kotun tarayya, shi ne alkalin da ya bada umarnin duka bangarorin a dakatar da komai biyo bayan karar da Sanata Melaye ya shigar har sai ta saurari karar tukuna. Sai dai hukumar zaben ta bukaci a jinginar da wannan umarni tare da yin korafi a kan alkalin alkalai na kasa bisa rashin mutunta hurumi ko damar da dokar kasa ta bai wa hukumar.
Shi ma lauyan da ke kare sanatan Mr. Nkem Okoro, ya ce lallai an mika masa takardar bukatun hukumar a Talatar da ta gabata, tare da cewa yana bukatar mako guda don yin nazari kafin ya ce wani abu. Bayan haka, mai shara’a Dimgba ya dage ci gaba da shara’a ya zuwa ranar Alhamis, 27 ga watan Yulin 2017.
A wani bayani mai yawan shafuka goma sha shida da hukumar INEC ta shirya don karfafa bukatun da ta gabatar, INEC ta ce korafin da aka gabatar a kan Sanata Melaye na rashin wakiltar yankinsu ne yadda ya kamata a majalisar tarayya.
Kazalika, hukumar ta ce kwanaki casa’in kacal hukumar ke da su daga ranar da ta samu wannan korafi, ta gudanar kuri’ar jin ra’ayoyin al’umar mazabar Kogi ta Yamma. Bayanin ya ci gaba da nuna cewa, daga ranar 21 ga watan Yunin 2017 wa’adin da kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa hukumar na kammala shirin kiranyen, zai cika ne ya zuwa 18 ga Satumba 2017.
Bugu-da-kari, cewa tuni hukumar ta fitar da jadawalin yadda harkokin kiranye za su gudana.
Sannan baya ga umarnin dakatar da shirin kirayen da kotu ta yi, ta kuma dage ci gaba da sauraron shara’ar zuwa 29 ga Satumban 2017 inda za a saurari korafin da Melaye ya shigar. Haka nan hukumar ta ce, ba a saurare ta ba kafin a kai ga bada umarnin dakatar da ita daga ci gaba da harkokinta.
A cewar INEC, umarnin duka bangarorin su dakatar da komai da aka bayar a ranar 6 ga Yuli, 2017, lamari ne da ya saba wa ’yancin sauraren wani batu kamar yadda yake kunshe cikin dokokin kasa a sashe na 36 (1). Kazalika, hakan ya take ‘yancin mai kokarin kare kansa wanda kundin tsarin mulki ya bada dama a sashe na 1 da na 69 na kundin dokokin kasa na shekarar 1999.
Dadin-dadawa, hukumar INEC na ra’ayin cewa bai kamata kotu ta bada wannan umarni ba musamman idan aka yi la’akari da yanayin korafin da aka gabatar mata da kuma wa’adin da dokar kasa ta amince mata na aiwatar da aikin kiranye. Ta ce, sashe na 69 na kundin tsarin mulkin kasar nan ya nuna cewa:
Abu na gaba shi ne, sai hukumar zabe ta gudanar da kuri’ar jin ra’ayoyin jama’ar mazabar da lamarin ya shafa a tsakanin kwana casa’in daga ranar da korafi ya zo gabanta, inda wadan suka cancanci kada kuri’a kadai za a lamunce wa su kada kuri’ar jin ra’ayin.
Da wannan ne hukumar INEC take rokon alkali da a dubi wannan lamari da idon basira wanda ke bukatar kulawa ta gaggawa sannan a yi abin da ya kamata. Idan dai za a iya tunawa, a ranar 23 ga watan Yunin da ya gabata ne Sanata Melaye ya maka hukumar INEC a kotu ta hannun lauyansa Chief Mike Ozekhome, inda ya bukaci kotu ta dakatar da INEC daga shirinta na neman yi masa kiranye.
A karar da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/587/2017, Melaye ya bayyana korafin da aka gabatar wa INEC a kansa a matsayin abu ne da aka zauna aka shirya.
Don haka, ya yi kira ga kotu da ta yi watsi da korafin da aka gabatar wa shugaban INEC, Farfesa Yakubu Mahmood. Haka nan, ya bukaci kotun da ta dakile shirin yi masa kiranye da INEC ta soma, saboda a cewarsa hakan ya take masa ’yancin da yake da shi na a saurare shi.