Hukumar Zabe Za Ta Fara Raba Katin Zabe A Watan Mayu

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewar, duk wanda ya yi rajisata, ya sa ran da zai amshi katin sa wanda za a fara badawa cikin watan Mayu na wannan shekarar 2008.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron tuntuba wanda aka yi bada dadewa ba, akan kwamitin zabe, tsaro, a hedikwatar Hukumar wadda ke Abuja.

Ya bayyana cewar ‘’ Muna ba duk wanda ya cancanci yin rajista tabbacin babu wanda za a bari baya , bugu da kari kuma, duk wadanda suka yi rajista tun shekarar 2017, su kwantar da hankalinsu saboda kuwa za su amshi rajistar su, cikin makon farko na watan Mayu  na 2018. Su kuma wadanda ke yin rajista  a wannan shekara ta 2018, za su amshi nasu kafin zabubbukan shekara ta 2018.

Shugaban ya yi kira da kuma jan hankalin jami’an tsaro  da kuma masu ruwa da tsaki a kan dukkan yadda al’amuran zabe ya kamata su tafi daidai, da cewar su hada kai, abin ma har ya zarce lokacin da za a yi zabubbuka, saboda kuwa ayyukan da ake cikin yin su, wani babban al’amari  ne kafin  a kai ga yin shi babban zaben.

Rajista domin zabe da kuma yin shi zaben lokacin zabe duk wata dama ce ta duk ‘yan Nijeriya, wanda kuma wadanda ba ‘yan kasa ba, da kuma wadanda ba su cancanta a yi masu ba wato kananan yara, basu da  damar yin haka kamar yadda doka ta hana yin haka gare su, saboda laifi ne.

 

Exit mobile version