Daga Zubairu M Lawal
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Nasarawa, Honorabul Ayuba Usman, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke garin Lafia.
Ya ce gudanar da sahihin zaben da za a yi a gundumar Gangara Tudu da ke Karamar hukumar Keffi, ya biyo bayan mutuwar Kansilan da ke wakiltar wannan mazabar.
Ya ce tun bayan mutuwar kansilan mazabar Gangara Tudu, margayi Adamu Saleh cikin watan Satunba da ya gabata al’umman mazabar ke zaune ba su da wakili a Majalisar Karamar hukumar Keffi.
Ya ce tuni Jam’iyyun da suke shirya fafatawa a zaben suka gabatar da sunayen ‘yan takarar su ga hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Nasarawa. Ta hanyar mallakar takardan tsayawa takara da suka yanka, ya bukaci wadanda ba su maido da ta su takardan ba su gaggauta maido da su kafin 24 ga wannan watan.
Shugaban hukumar zaben, Honorabul Ayuba Usman wanda ya ce zaben zai gudana cikin kwanciyar hankali saboda duk hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da tsaro a lokacin zaben an shirya masu.
Sannan zabe ne da zai gudana cikin gaskiya da yin adalci ga duk dan takarar da ya yi nasara.
Ya kara da cewa hukumar zaben ta sanar da ranar 19/10/2020 ‘yan takarar su fara yakin neman zaben a gundumar Gangara Tudu.
Sannan ya shawarci ‘yan takarar dukkan jam’iyyun da su gudanar da yakin neman zaben a cikin tsari ba tare da yarfe ko abin da zai kawo tashin hankali ba.