Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Hukumomin Saudiyya Sun Cancanci Yabo, La’akari Da Yadda Matakansu Suka Taka Rawa Wajen Dakile COVID-19 Tsakanin Mahajjata

Published

on

A jiya Litinin ne, mahajjata suka kammala aikin hajjin bana, inda suka yi wa garin Makkah bankwana bayan sauke faralin.

Aikin hajjin na bana ya zo da gagarumin sauyi, saboda zuwansa a lokacin da duniya ke fuskantar kalubalen da ta shafi kowa da kowa ba tare da la’akari da launi ko kabila ko yanki ba, lamarin da ya sa ya gudana cikin wani yanayi na ban mamaki da ba a taba gani ba.
Sai dai abun farin ciki shi ne, tsauraran matakan da kasar Saudiyya ta dauka da nufin kare lafiyar mahajjatan, sun cimma manufofinsu, domin kwalliya ta biya kudin sabulu, kasancewar an yi an gama ba tare da samun ko da mutum guda da ya kamu da cutar COVID-19 ba.
Hukumomin Saudiyya sun cancanci yabo domin sun dauki tsauraran matakai. Ko kayyade adadin mahajjata kadai da aka yi, ba abu ne mai sauki ba, la’akari da cewa, a kowacce shekara, aikin hajjin da ya ja hankalin mutane kimanin miliyan 2.5 daga kasashen duniya daban-daban a bara, wanda ke kara samar da kudin shiga da ayyukan yi ga al’umma da gwamnatin kasar, sai kuma a bana aka kayyade adadin zuwa mutane dubu 10, kuma wadanda ke zaune a cikin kasar kadai, da nufin tabbatar da matakin nisantar juna.
Baya ga haka, hukumomin kasar sun yi namijin kokari wajen aiwatar da tarin matakai, ciki har da gwajin cutar kafin aikin hajjin da killace su bayan kammala sauke faralin da bibiyar lafiyarsu yayin da suke ibadar da kuma kasa aikin zuwa rukuni rukuni, da sauransu, duk dai domin tabbatar da lafiyarsu.
Babu wani mataki mafi dacewa fiye da wanda aka dauka. Duk da cewa aikin hajjin farilla ne kuma daya daga cikin ginshikan addinin musulunci, addinin bai yarda da mabiya su sanya lafiyarsu cikin hadari ba. Maimakon soke aikin hajjin baki daya, sai gwamnatin Saudiyya ta dauki wadancan matakai, wadanda kuma suka taka rawa gaya wajen ganin cutar ba kawo cikas ga aikin sauke faralin ba.
Advertisement

labarai