Connect with us

MATASAN ZAMANI

Hukuncin Daurin Rai-Da-Rai Ya Dace Ga Masu Aikata Fyade

Published

on

A wani bincike na baya-bayan nan da aka fitar, a cikin duk mata 4, daya ta taba fuskantar cin zarafin fyade a lokacin da ta ke ƴar kasa da shekaru 18, wannan shi ke kara nuna mana cewa matsalar fyade ta zama annoba wacce ta ke bukatar a taka mata birki ta hanyar yanke wa duk wanda ya aikata hukuncin daurin rai da rai a Nijeriya.

Bayyanar rahotannin yi wa mata fyade ba wani sabon abu ba ne a Nijeriya, domin kuwa a kusan kullum sai an samu labarin an yi wa mace baliga ko yarinya karama fyade a wannan kasa. Ba ka yi kuskure ba idan ka ce matsalar fyade ta zama ruwan dare mai gama duniya a wannan kasa ba, duba da yadda kusan kowacce Jiha da karamar hukuma da mazaba an taba samun rahoton “an yi wa mace fyade ko dai mace baliga ko yarinya karama. Wani karin abin haushi ta tashin hankali a wasu lokutan sai ka samu an yi wa mace fyade kuma an kashe ta, a wasu lokutan sai ka samu mace daya baliga ko yarinya karama sama da namiji daya ne ya lalata ta, wata maza uku zuwa sama duk sun yi mata fyade a lokaci guda.

 

Nijeriya kasa ce wacce ta ke da dokoki kan ƴan fashi da makami da masu satar dukiyar kasa da masu kashe rayukan mutane haka kawai da sauran masu aikata miyagun laifuffuka. Duk da cewar akwai dokoki akan masu aikata fyade, sai dai dokokin ba su da karfin da za su kawo karshen matsalar. Mu na bukatar a samar da manyan dokoki masu karfi da tasiri wadanda za su taimaka wajen magance matsalar fyade kafin matsalar ta zame mana al’ada ta yi girman da za ta gagara.

Fyade aiki ne na dabbanci da rashin hankali, domin in ba dabbanci da rashin hankali ba, babu yadda za ayi mutum mai lafiyayyen hankali da tunani ya kama mace baliga batare da yardar ta ba ya yi mata lalata, da kuma yarinya karama wacce ba ta ma mallaki hankalin kanta ba, amma mutum baligi ya kamata ya yi mata lalata. Wannan aiki ne na dabbanci da rashin hankali wanda ya ke bukatar daukar mataki mai tsauri akan duk masu aikatawa.

A wani bincike na baya-bayan nan da aka fitar, a cikin duk mata 4, daya ta taba fuskanar cin zarafin fyade a lokacin da ta ke ƴar kasa da shekaru 18. Wannan shi ke kara nuna mana cewa matsalar fyade matsala ce mai girman gaske wacce ta zama annoba, ta ke cigaba da habaka, ya kamata a taka mata birki. Dokokin da mu ke da su a yanzu ba su gamsar ba. Na taba karanta dokar daurin shekara daya ko zabin biyan tara ta 2,000 a matsayin hukuncin wanda ya aikata lefin fyade a daya daga cikin Jihohin Nijeriya. Wannan hukunci ba hukunci ba ne, ya yi kadan ga mutumin da ya lalata rayuwar mace ya sanya ta cikin tashin hankali da rashin nutsuwa.

 

Wasu daga cikin masu aikata fyade su kan tare mace a hanya a inda babu kowa ko su kamata su sa ta a cikin abin hawa musamman mota su tafi da ita inda duk su ke so su yi mata fyade ta karfi. Wasu kuma su kan ribaci mawuyacin halin da mace ta ke ciki su bukaci temaka mata ko ita ta nemi gudunmawarsu sai su yi mata fyade.

Babban abin da ya kamata ayi ga duk wanda aka kama da lefin ya yi wa mace baliga ko yarinya karama fyade shi ne a yanke masa hukuncin shekaru 20-30 ko daurin rai da rai a gidan kaso. Domin duk wacce aka yi wa fyade an jefa rayuwarta ne cikin hatsari, za ta rayuwa ne a cikin fargaba da tashin hankali da fuskantar kyama daga jama’a in aka yi rashin sa’a ma sai a rasa wanda zai aure ta shikkenan an kashe mata rayuwa wata bakin ciki da tashin hankali ne zai yi sanadiyyar mutuwarta, wata kuma guba ma za ta sha ta mutu saboda bakin cikin halin da ta ke ciki. Amma idan ya kasance duk wanda ya aikata fyade za a ajiye shi a gidan yari har kwanansa ya kare to ba makawa za a samu nasarar ceto rayuwar ƴaƴa mata daga fuskantar cin zarafin fyade. In mutum daya ya aikata fyade a daure shi rai da rai, haka zalika ko da mutum dari ne za su taru akam mace daya su yi mata fyade, to duk a daure su rai da rai.

Wannan zai samu ne idan ya kasance gwamnati ta ba da hadin kai wajen yin dokar, sannan su ma matan da wanna bala’i na fyade ya ke afkawa da iyalai su dena boyewa su na shigar da kara domin a hukunta wanda duk ya aikata. Lauyoyi su rika ba da gudunmawa wajen tsayewa duk wacce aka yi wa fyade ko da ba ta da kudi su yi mata gata, haka zalika al’ummar da su ke da shaida kan lefin fyade su dena kin zuwa ba da shaida, su ma iyalai ko iyaye su dena duba ƴan uwantaka ko zumunci balle ace ayi sulhu a gida, sannan alkalai su rika ba da gudunmawa wajen daukar kes din fyade da muhimmanci, su dena jinkirta shari’a ko karban na goro su gaggauta karban hujjoji cikin hanzari duk wanda aka samu da lefin fyade a gaggauta yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso ko mai rauninsa kuma komai gatansa a Nijeriya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: