Hukuncin Kotu: Za A Biya el-Rufa’i Naira Miliyan 10 Kan Bata Masa Suna

Daga Sulaiman Ibrahim,

Wata babbar kotun jihar Kaduna ta umurci kamfanin buga jaridu na Today Publishing, Mai kamfanin jaridar The Union, da ya bayar da hakuri tare da biyan Naira miliyan 10 bisa zargin bata sunan Gwamna Nasir el-Rufai.

Gwamna El-Rufai ya kai karar kotu ne a shekarar 2015 bayan kamfanin na Today’s Publishing Company Ltd. ya buga labarin bayyana kadarorin sa, a karar mai lamba KAD/KDH/285/15, Gwamnan ya ce labarin karya ne.

Justice M.L. Muhammed na babbar kotun jihar Kaduna wanda ya yanke hukuncin, ya umarci wadanda ake kara da su biya El-Rufai kudi naira miliyan 10 a matsayin diyyar batanci da kuma bayar da hakuri wanda dole ne a wallafa bayar da hakurin a jaridun kasar Nijeriya.

Idan dai za a iya tunawa, lamarin ya biyo bayan wani labari ne a shafin farko da aka buga a jaridar The Union a ranar 2 ga watan Yulin 2015, inda ya bayyana cewa gwamnan ya bayyana kadarorinsa da suka kai Naira N90bn da kuma manyan gidaje 40.

Exit mobile version