Hukuncin Kotun Koli: Allah Ya Isa Tsakaninmu, Cewar Abba Gida-gida

Dan takarar Jam’iyyar PDP a zaben kujerar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda a ka fi yi wa lakabi da Abba Gida-gida, ya bayyana cewa, a yanzu Allah ya isa ce tsakaninsu da Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bisa hukuncin da Kotun Koli ta yanke, wanda ya tabbatarwa da Gandujen halascin lashe zaben kujerar gwamnan da a ka gudanar cikin watan Maris na 2019.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun dan takarar PDP din, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai jim kadan bayan sanar da tabbatar nasarar ta gwamnan na Kano.

To, amma shi kuma Gwamna Ganduje a nasa jawabin da ya gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Kano a gaban magoya bayansa, ya yi kira ga ’yan adawar nasa ne da su mayar da takobi cikin kube, domin shi yanzu ya yafe mu su dukkan abubuwan da su ka faru tsakaninsu a lokacin yakin neman zabe.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Litinin din da ta gabata, 20 ga Janairu, 2020, ne Kotun Kolin Nijeriya karkashin jagorancin Maishari’a Sylbester Ngwuta ta yanke hukuncin cewa, Ganduje ne halastaccen zababben Gwamnan Jihar Kano a zaben da a ka gudanar bara, domin dan takarar PDP da ita kanta jam’iyyar ba su iya kawo kwararan hujjoji gaban kotu, wadanda za su iya sa wa a soke zaben ko a bai wa nasu dan takarar ba.

Don haka ne Kotun Kolin ta ce, kananan kotunan da su ka amince da Ganduje a matsayin yabci halak (wato Kotun Zabe da ta Daukaka Kara) sun yi daidai.

To, amma a martanin da Abba Yusuf ya mayar ya kwatanta wannan hukunci a matsayin abin takaici ga dimukradiyyar Nijeriya.

“Hukuncin da a ka aiwatar yau kan takarar kujerar gwamnan jihar Kano ya kara fito da irin tsananin hadin bakin da a ke shi wajen aikata fashi da makami ga dimukradiyyar Nijeriya,” in ji shi.

Ya kuma kara da cewa, “mun yi tsammanin cewa Kotun Koli za ta yi adalci bisa la’akari da irin kwararan hujjojin da zakakuran lauyoyinmu su ka gabatar a shari’ar, to amma babu wanda zai iya hango irin karfin zaluncin da a ka hada hannu da shi a ka aikata wa al’ummar Kano fashi da makami da tsakar rana haka.”

Daga nan sai ya ce, “yanzu dai mun ga irin iyaka makurar abinda za su iya aikatawa. To, sai su jira hukuncin Allah, wanda ba za su iya kauce ma sa ba.”

To, amma a martanin Gwamna Ganduje, ya yi jan hankali da cewa, ba bakon abu ba ne shirya murda-murda da makirci a siyasar duniya. Sai dai kuma a kasashen da a ka waye, a na sanya cigaban kasa ne a gaba kurum bayan da a ka kammala sha’anin siyasar zabe.

Daga nan sai ya ce, shi dai ya yafe wa kowa laifin da ya yi ma sa a lokacin yakin neman zaben, hatta jagoran Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, da daukacin mabiyansa da kuma ita kanta jam’iyyar PDP, wadanda su ne jagaban adawa da gwamnatinsa.

Ya ce, lallai ne yanzu su zo su hada hannu da shi, domin cigaban al’ummar jihar Kano, idan har da gaske su ke yi cewa, bunkasar jihar ne a gabansu.

Daga na sai ya gode wa sarakuna, malamai da sauran masu ruwa da tsaki a jihar bisa irin rawar da su ka taka a lokacin da a ka shiga badakala da rudanin siyasar 2019 a jihar ta Kano.

A ka’idar fasalin dokokin Nijeriya, wannan hukunci na Kotun Koli dai ya kawo karshen duk wata jayayya kan zaben kujerar gwamnan jihar kenan. Sai dai kuma a jira 2023 ga mai yawan rai.

Exit mobile version